Za a yi zaben Shugaban Kasa a Nijeriya ranar 20 ga Fabrairun 2027, in ji INEC

Waɗannan ranaku sun yi daidai da ana tsakiyar yin azumin watan Ramadana na shekara mai zuwa ke nan yayin da zaɓukan gwamnan za su faɗa a ranakun shirin sallah.

By
INEC / Nigerian Government

Hukumar zaɓen Nijeriya (INEC) ta fitar da jadawalin zabukan shekarar 2027 da za a yi a ƙasar, inda ta ce na Shugaban Kasa zai kama ranar 20 ga Fabrairu.

A bisa jadawalin, za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa a ranar Asabar, 20 ga Fabrairu, 2027. Zaben Gwamna da na Majalisar Dokoki ta Jiha zai biyo bayan makonni biyu bayan haka a ranar Asabar, 6 ga Maris, 2027.

Waɗannan ranaku sun yi daidai da ana tsakiyar yin azumin watan Ramadana na shekara mai zuwa ke nan yayin da zaɓukan gwamnan za su faɗa a ranakun shirin sallah.

Hukumar ta kuma bayyana lokutan yakin neman zabe na jam'iyyun siyasa da 'yan takara. Yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki na ƙasa zai fara daga 18 ga Nuwamban 2026, zuwa 19 ga Fabrairun 2027.

A halin yanzu, yakin neman zaɓen gwamna da na 'yan majalisar jiha zai fara a ranar 15 ga Disamban 2026, kuma ya ƙare a ranar 5 ga Maris, 2027, daidai sa'o'i 24 kafin ranakun zaɓe.

A matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen zaɓen, INEC ta sanar da cewa za a fara rijistar masu zaɓe akai-akai (CVR) a watan Afrilun 2026 kuma za a ƙare a watan Janairun 2027, wanda zai ba wa 'yan Nijeriya da suka cancanta isasshen lokaci don yin rijista ko sabunta bayanan masu zaɓe.

Ana sa ran jam'iyyun siyasa za su gudanar da zaɓen fidda gwani tsakanin 1 ga Yuli zuwa 30 ga Satumban 2026, bayan haka dole ne su gabatar da jerin 'yan takararsu ga hukumar tsakanin 1 ga Oktoba zuwa 31 ga Oktoban 2026.

Za a sakin jerin sunayen 'yan takara na ƙarshe a ranar 15 ga Nuwamban 2026.

INEC na neman naira biliyan 873 don gudanar da zaɓukan shekarar 2027

Tun da fari a ranar Alhamis, hukumar zaɓen Nijeriya (INEC) ta yi hasashen cewa za ta buƙaci naira N873,778,401,602.08 domin gudanar da zaɓen shekarar 2027.

Shugaban INEC Joash Amupitan ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da kasafin kudin hukumar na shekarar 2026 da kuma cikakken bayani game da iya kudin da za a kashe kan zaɓukan ƙasa na 2027, a gaban kwamitin haɗin-gwiwa na majalisar dokokin ƙasar kan harkokin zaɓe.

Bayani dalla-dalla na kasafin kuɗin ya nuna cewa kuɗin da za a kashe kan ayyukan zaɓukan sun kai N375,748,195,271.47, yayin da kuɗin gudanarwa na zaɓe ya kai N92,311,591,396.58.

Hukumar ta kuma yi hasashen cewa za ta kashe naira N209,205,589,977.70 kan fasaha na zaɓe, lamarin da ke nuna tanadi na tsarin amfani da komfuta da abubuwa makamancin hakan a zaɓen.

Bugu da ƙari, kudin da ake hasashe za a kashe kan manyan abubuwa a zaɓen zai kai naira N154,904,529,641.94.

Waɗannan hasashen abubuwa huɗun jumullarsu ne ya kama N832,169,906,287.69.

INEC ta kuma haɗa kuɗaden wasu abbubuwan daban-daban da ta yi hasashen za su ci naira N41,608,495,314.39, lamarin da ya mayar da jumullar kuɗaɗen da za kashe a zaɓukan shekarar 2027 gabaɗaya zuwa N873,778,401,602.08.

Amupitan ya bayyana cewa kasafin kuɗin zaɓen ya sha bamban da kasafin kuɗin hukumar na shekarar 2026 wanda ya kai naira biliyan N171, wanda zai ɗauki nauyin ayyuka na yau da kullum, ciki har da zaɓukan cike-gurbi da na zaɓukan da za a yi a lokacin da ba na zaɓukan ƙasa ba.

A lokacin zaman, ‘yan majalisa sun nuna damuwa game da hanyoyin samun kudin da kuma ƙaddamar da muhimman tanade-tanaden dokar zaɓen Nijeriya da aka gyara, musamman batun tura sakamakon zaɓe ta intanet.

Shugaban kwamitin na haɗin gwiwa kan batutuwan zaɓe, Sanata Samuel Lalong, ya bayyana cewa majalisar dokokin ƙasar za ta yi cikakken bincike kan kasafin kuɗin ta amince zai iya ba da damar gudanar da zaɓuka a fadin ƙasar.

Ya jaddada cewa yayin da INEC ta gabatar da kasafin kudinta, aikin amincewa da kuma tabbatar da kasafin kudin ya rataya ne a kan ɓangaren dokoki.

Kazalika kwamitin ya kuma nuna cewa yana shirin sake yin duba kan kuɗaɗen matasa masu yi wa ƙasa hidima da za a tura domin ayyukan zaɓukan, bayan hukumar da ke kula da shirin yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta nemi ƙarin tallafi na kudi.

A ƙarƙashin buƙatar, kowane mai yi wa ƙasa hidima zai karɓi naira N127,000, tare da naira N4,500 na cin abinci da kuma naira N5,000 na horaswa cikin kwanaki fiye da biyar.

Kimanin matasa masu yi wa ƙasa hidima 450,000 ne ake tsammanin za a tura ayyukan a lokacin zaɓukan ƙasa mai zuwa.