'Yan Nijeriya miliyan 45 suna bahaya har yanzu a waje — Ministan Muhalli
Fiye da mutane miliyan 45 a Nijeriya har yanzu suna yin bahaya a waje, kuma kusan kashi 25 cikin 100 na al'ummar ƙasar ne kawai suke da damar samun wurare masu tsafta da aka ware don bahaya, a cewar ministan muhalli na Nijeriya
Nijeriya na fuskantar matsalar tsaftar muhalli mai tsanani, inda fiye da 'yan ƙasar miliyan 45 ke ci gaba da yin bahaya a waje, in ji Ministan Muhalli na Nijeriya Mallam Balarabe Lawal.
Ministan ya bayyana haka ne a Abuja a yayin taron manema labarai kan bikin Ranar Banɗaki ta Duniya ta 2025, wanda aka yi wa take da "Tsabtace Muhalli a Duniyar da ke Canzawa" ƙarkashin maudu’in ‘‘Muna Buƙatar Bandaki a ƙullum.’’
Malam Lawal ya yi da yanayin da ake ciki a matsayin wata babbar matsala ta lafiyar al’umma da kuma ƙalubane na muhalli.
Ministan, wanda Sakataren Dindindin, Mallam Mahmud Kambari ya wakilta, ya ce kashi 25 cikin 100 na 'yan Nijeriya ne kawai suke da damar samun wurare masu tsafta da aka ware, don yin bahaya duk da ƙoƙarin da duniya ke yi na inganta tsaftar muhalli.
"A faɗin duniya, kimanin mutane biliyan 4.2 ba su da damar yin bahaya a wuraren da aka ware mai aminci.
“A Nijeriya kuwa, sama da mutane miliyan 45 har yanzu suna yin bahaya a fili, kuma kashi ɗaya cikin huɗu na al'ummar ƙasar ne kawai ke amfani da wurare tsaftacce da aka ware masu aminci," in ji shi.
Ministan ya koka kan yadda makarantu, da asibitoci, da cibiyoyin gwamnati da dama ba su da bandakuna kwata-kwata ko kuma suna amfani da waɗanda ba a kula da su sosai.
Ya kuma ƙara da cewa, har yanzu cibiyoyin birane da dama suna dogaro ne kan tsarin magudanar tattara shara wadanda suka gaza, lamarin da ke janyo kwararar ruwan datti zuwa cikin koguna da rafuka - yanayin da ke mummunan tasiri ga lafiyar dan’adam.
A cewar ministan, rashin tsaftar muhalli na ci gaba da haifar da barkewar cutar kwalara da gudawa da taifod da cututtukan da ke haifar da tsutsitsi cikin mutum da ke kashe dubban ‘yan Nijeriya kowace shekara, musamman yara 'yan ƙasa da shekara biyar.
Ya kuma yi gargaɗin cewa rashin tsaftar muhalli yana taimakawa wajen hana ƙwayoyin cuta mutuwa kuma yana haifar da cikas ga ci gaban Nijeriya na shirin SDG 6.2.