An gano ƙwarangwal ɗin wata babbar dabbar dinosaur mai kama da tsuntsu a Hamadar Nijar

Amma a wannan karon, an gano burbushin halittun ne a can ƙarƙashin ƙasa, ɗaruruwan mila-milai daga inda teku mafi kusa zai kasance.

By
Masana kimiyya sun gano ƙwarangwal ɗin wani babban tsuntsu mai kama da dinosaur a Hamadar Nijar / AFP

A cikin hamadar Nijar, masana kimiyya sun gano wani nau'in dabbar dinosaur da ba a san ta ba.

Kimanin shekaru miliyan 95 da suka wuce, Spinosaurus -- wata babbar dabba mai zagayayyen kai da kafta-kaftan haƙora ta rayu a nahiyar Afirka.

Masu bincike sun tono burbushin halittu nau’in Spinosaurus mirabilis -- ko "hell heron", kamar yadda Paul Sereno, masanin burbushin halittu na Jami'ar Chicago kuma babban marubucin binciken da aka buga a mujallar Science ya faɗi sunanta.

"Duba tsawon ƙoƙon kan, da tsawon wuyan da na hannun, kana gani ka san ya yi kama da tsuntsun zalɓe."

Dabbar dinosour nau’in Spinosaurus mirabilis ta rayu a lokacin da yankin Sahara na yau ya kasance daji ne da kuma koguna. A baya can, an fi samun dabbar spinosaurid fa gabar tekuna a Kudancin Afirka.

Wasu masana kimiyya sun yi tunanin cewa waɗannan halittu masu cin kifi na iya kasancewa dabbobin ruwa ne, suna yawo a cikin ruwa mai zurfi don kama abin farauta.

Amma a wannan karon, an gano burbushin halittun ne a can ƙarƙashin ƙasa, ɗaruruwan mila-milai daga inda teku mafi kusa zai kasance.

"Ina tsammanin dabba ce da za ta iya shiga cikin ruwa cikin sauƙi," in ji Sereno.

"Amma ban yi tsammanin mai nutsewa ba ce, ban yi tsammanin ta ƙware a iyo ba."

Fara bincike

An fara binciken ne a shekarar 2019 a cikin hamadar Sahara, inda masanin ilimin ƙasa na Faransa Hugues Faure ya ce ya sami haƙorin wata babbar dabba ta Carcharodontosaurus a shekarun 1950.

"Muna da wasu abubuwa da Faure ba zai taɓa mafarkinsu ba. Muna da na’urar GPS mai gano wurare, muna da jiragen sama marasa matuƙa da kuma ingantattun motoci," in ji Sereno.

Ba a gano komai a yashin ba, kuma hakan ya ɓara tan tawagar inda suka koma sansaninsu.

Amma wani mutum ɗan ƙabilar Abzinawa sanye da baƙar riga mai launin ruwan kasa ya kusanci tawagar Sereno a kan babur, yana iƙirarin cewa ya san inda "manyan ƙasusuwa" suke.

Bayan doguwar tafiya a cikin hamada, Sereno ya damu cewa "sun yi kuskure".

"Mun yi dariya muna cewa, shin har yanzu muna Nijar? Ina nufin, mun yi tuƙi na kwana ɗaya da rabi har sai da ba mu da sauran man fetur domin ba za mu iya komawa ba."

Amma daga ƙarshe sun isa wani wuri mai nisa inda aka tono "manyan ƙasusuwa... da na taɓa gani a rayuwata" daga ƙasa.

A can nesa da hamada, masu binciken sun kaɗu da ganin ƙwaragwal ɗin dabbar mai tsawon ƙafa shida, da ƙton muƙamuƙi, da manyan haƙora, da kuma tushen kabarin.

A shekarar 2022, Sereno ya dawo tare da tawagar mutane 100 da masu gadi 64 na Nijar don tono "wurin a ƙasa".

Sun tono ƙarangwal din mai haɗe da ƙafafu da sauran sassan jiki.

“Wani abu ne da ba mu taɓa ganin irinsa ba,” in ji Sereno.

Wasu sai da suka yi kuka, in ji shi saboda ganin wannan abin al’ajabi.

“Abin ya yi kama da hoton dijital na dabbar dinsour tana zaune a cikin tantii a tsakiyar Sahara.

Tawagar ta fahimci cewa “wani sabon nau’in dabba ce… kuma zai kasance wani abu na tarihi da aka gano wanda ba a taɓa samun irinsa ba.”