| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Ghana ta buƙaci taimakon MDD don warware batun cinikin bayi saboda ƙarfafa ƙoƙarin neman biyan diyya
Wakilin Ghana a Majalisar Dinkin Duniya, Samuel Yao Kumah, a ranar Litinin ya bukaci kasashe mambobin Majalisar da su goyi bayan kudirin da ke neman a amince da cinikn bayi ta taekun atlantika a matsayin ‘laifi mafi girma ga bil’adama’.
Ghana ta buƙaci taimakon MDD don warware batun cinikin bayi saboda ƙarfafa ƙoƙarin neman biyan diyya
Tsawon lokaci, kasashen Afirka na ta matsa lambar samun diyya saboda cinikin bayi na zamanin mulkin mallaka. / Others / Others
24 Maris 2026

Wakilin Ghana a Majalisar Dinkin Duniya, Samuel Yao Kumah, a ranar Litinin ya bukaci kasashe mambobin Majalisar da su goyi bayan kudirin da ke neman a amince da cinikn bayi ta taekun atlantika a matsayin ‘laifi mafi girma ga bil’adama’, yana mai cewa hakan zai karfafa kokarin da ake yi na ganin an biyya diyya.

Matakin na da manufar neman goyon bayan kokarin bukatar a biya diyya da ‘yan uwanmu na Caribbean,’ ke jagoranta, Kumah ya fada wa taron ‘yan jarida na Afirka kafin Shugaban Kasar Ghana John Dramani Mahama ya kawo kudirin ga Babban Zauren Majalisar ranar Laraba.

Ya jaddada cewa kudirin ba ya neman “kimanta shan wahala ko rage girman bala’o’in tarihi,” sai dai yana bayyana ‘muhimman gabobi na tarihi’ da suka sake fasalin mutumtaka da kafa tsarin da ke ci gaba da wanzar da rashin daidaito a duniya a yau.

“Tare da amincewa da wadannan gasgatattun al’amura na tarihi, kasashen duniya na kara karfafa ikonsu wajen magance kalubalen da ake fuskanta a yau wanda ya samo asali daga abubuwan da suka faru a baya,” in ji shi.

Amincewa ta siyasa da tarihi

Kumah ya ce kudurin ya amince da fataucin mutane da kuma bautar da 'yan Afirka a matsayin wani sabon rikici na tarihi wanda ya kawo nun wariya a yadda ake juya duniya a yau.

Ya jaddada cewa irin wadannan kudurorin na Majalisar Dinkin Duniya kayan aiki ne na siyasa, ba hukunce-hukuncen shari'a ba, kuma ba za su iya samar da manyan matakai na laifuka ba. Matakin ya kunshi amincewa da siyasa da tarihi maimakon rarraba dokoki.

Duk da cewa kudurin bai yi cikakken bayani kan diyya ba, Kumah ya ce Ghana da abokan huldarta suna da manufar samar da tushe ga wasu shirye-shiryen biyan diyya.

Ya kuma lura da cewa an yi amfani da dokar a tarihi don ba da hujja ga bautar 'yan Afirka da kuma tilasta wariyar launin fata tsawon sama da ƙarni biyar.

Ya ce, kokarin gane wannan gaskiyar tarihi sau da yawa na fuskantar batutuwan shari'a wadanda "ke haifar da barazanar toshe muryoyi da kuma boye gaskiyar tarihi."

Kumah ya kara da cewa "Bai kamata doka ta sake zama kare tabbatar da gaskiya ba,"