Gargadin shugabannin Afirka kan cin abinci a makare da illolin shan siga da giya
AFIRKA
4 minti karatu
Gargadin shugabannin Afirka kan cin abinci a makare da illolin shan siga da giyaShugabannin sun jaddada cewa cin abincin dare a makare da yawan shan siga da barasa, da cin burodi da shinkafa su ne manyan abubuwan da ke haifar da cututtuka masu kisa a kasashen Afirka
Shugabannin ƙasashen Uganda da Rwanda da kuma Ghana

Shin ko san cewa cin tuwon dare a makare zai iya zama sillar kamuwa da ciwon siga (diabetes)?

Tabbas, cin abincin dare a makare da shan kayan zaki da rashin motsa jiki suna cikin dalilan da suke haifar da cututtuka kamar ciwon siga da cancer da ciwon zuciya da hawan jini da sauransu.

 Kuma wadannan manyan cututtuka masu hadarin gaske suna cikin dalilan da ke yin ajalin dubban mutane a duk shekara a kasashen Afirka.

 Saboda haka ne wasu shugabannin kasashen Afrika guda uku — wato Ghana, Rwanda da kuma Uganda — suka fito fili suna jan kunnen jama’a game da yadda wadannan cututtuka suke lalata lafiyar al’ummarsu.

 Shugabannin sun jaddada cewa cin abincin dare a makare da yawan shan siga da barasa, da cin burodi da shinkafa su ne manyan abubuwan da ke haifar da cututtuka masu kisa a kasashen Afirka.

Idan muka fara da Shugaba John Dramani Mahama na Ghana, wanda ya gargadi al’ummar kasarsa kan yawan amfani da siga da cin abincin dare a makare, lokacin kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiya kyauta ta farko (Free Primary Healthcare Programme), ya gargadi ’yan kasar da su daina cin abinci mai nauyi bayan karfe 7:00 na dare.

Na’ukan abincin da ya bukaci ’yan kasarsa su kauracewa ci bayan karfe 7:00 na dare su ne fufu, banku, da akple. Kazalika ya yi gargadin cewa yawan shan siga yana daya daga cikin dalilan da suke haddasa ciwon kansa. Ya ce babu laifi idan mutum zai ci wadannan nau’ukan abinci da rana.

 Sannan ya ce cin abinci mai nauyi da daddare tare da rashin motsa jiki suna kara hatsarin kamu da ciwon hawan jini (BP), da ciwon siga da yin mummunar kiba da sauran cututtuka masu hadari.

 Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa kimanin mutum 200,000 ne ke kamuwa da ciwon siga duk shekara a kasar Ghana. Sannan WHO ta ce mutum kimanin 17,000 ne mutuwa sanadin ciwon kansa a kasar a duk shekara.

 Watakila saboda wannan mummunar barnar da wadannan cututtuka biyu suke yi wa al’ummar kasar Ghana ne ya sa shugaban yake jan hankalin jama’ar kasar don su tashi tsaye wajen kula da lafiyarsu.

 Shugaban kasa na biyu a baya-bayan nan da ya bayar da shawara kan kula da lafiya shi ne Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame, wanda ya gargadi matasan kasar kan illolin da ke tattare da shan giya.

 Yayin da yake jawabi ga matasa a cibiyar horar da dakarun soji ta Gabiro, Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame, ya tsawatar wa matasa kan illolin shan giya.

 Kagame ya jaddada cewa giya na lalata makomar matasa kuma tana halaka su, sannan tana kashe rayuwarsu.

 Masana kiwon lafiya sun gano cewa shan giya yana haddasa dimbin matsaloli ga lafiyar dan Adam ciki har da ciwon hanta da zuciya da kuma cancer.

 Shugaban kasa na uku da ya yi magana kan kula da lafiya shi ne Yoweri Museveni na kasar Uganda wanda shi kuma ya yi gargadi kan cin shinkafa da burodi.

 Shugaba Museveni, a yayin wani taron jam’iyyarsa ta siyasa, ya bayyana cewa rabonsa da cin shinkafa tun lokacin da ya dawo daga gudun hijira a kasar Tanzaniya a shekara ta 1979, wato kimanin shekaru 50 kenan da suka wuce.

 Museveni ya ce ya fi sha’awar abincin gargajiya na gida kamar rogo da gero da gyada da ayaba saboda suna kunshe da sinadaran gina jiki da ke kara lafiyar jiki.

 Daga nan shugaban ya shawarci mutane da su guji abincin da ba na gargajiya ba, kamar shinkafa da burodi.

 Burodi na daga cikin abincin da masana kiwon lafiya da dama suke gargadi kansa a ’yan shekarun nan saboda yadda take jawo ciwon siga.

 Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce akwai kimanin ’yan Uganda mutum 369,100 zuwa 700,000 da a halin yanzu suke fama da ciwon siga, kuma kusan kaso 90 cikin 100 daga cikinsu ba su san sun kamu da cutar ba.

 Watakila saboda wannan dalilin ne ya sa Shugaba Museveni, mai shekaru 81, yake kiraye-kirayen a kauracewa cin burodi da shinkafa.