Sudan na fuskantar mummunar matsalar ƙarancin abinci, yayin da yaƙin da ake yi a ƙasar kusan shekaru uku da rabi ke ci gaba da haddasa tashin farashin kayan masarufi, har ta kai ga miliyoyin mutane na fama da wahalar sayen abinci mafi sauƙi kamar burodi.
A babban birnin ƙasar, Khartoum, farashin burodi ya ninka cikin mako guda, inda ya tashi daga fam 250 zuwa 500 na Sudan. A halin da ake ciki, ƙarancin alkama da man fetur ya tilasta wa gidajen yin burodi da dama rufe kasuwancinsu.
Wata mata mai shekaru 44, Sawsan Mahmoud, mai yara uku, ta ce ita da mijinta yanzu suna kashe kusan dukkan albashinsu wajen sayen burodi, lamarin da ya tilasta musu rage yawan burodin da suke ci a kullum.
Ta ce yanzu suna cin burodi sau ɗaya kawai a rana, kuma suna ware fam 900,000 na Sudan, kwatankwacin dala 88, a duk wata domin sayen sa.
Matsalar ta ƙara ta'azzara sakamakon faɗuwar darajar kuɗin ƙasar, inda fam ɗin Sudan ya rasa kusan kashi 25 cikin 100 na darajarsa idan aka kwatanta da dalar Amurka a cikin watan da ya gabata.
A lokacin da yaƙin ya ɓarke a shekarar 2023, ana musayar dala ɗaya kan kusan fam 500 na Sudan. Sai dai a baya-bayan nan farashin dalar ya haura fam 10,500 kafin daga bisani ya ɗan sauka.
Ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa sun yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar yunwa mai tsanani ta bazu a ƙasar, bayan da aka riga aka ayyana aukuwar matsalar yunwa a wasu sassan Sudan.
Kimanin mutane miliyan 20 ne ke fama da matsanancin ƙarancin abinci, yayin da rahotanni suka nuna cewa talauci ya ƙaru zuwa kashi 80 cikin 100 a al'ummar ƙasar.
Gidajen Burodi na Fuskantar Barazanar Rufewa
Ƙarancin garin fulawa ya kuma ƙara wa gidajen yin burodi da suka rage ayyuka wahalar ci gaba da harkokinsu.
Mohammed al-Fateh, mai gidan burodi a Khartoum, ya ce gidajen burodi da dama sun rufe saboda rashin samun garin fulawa a kasuwa.
Ya bayyana cewa wasu 'yan kasuwa kan shafe kwana ɗaya ko biyu suna jira a wuraren sayen fulawar, amma daga ƙarshe su koma gida babu komai.
A unguwar Al-Azhari da ke kudancin birnin, wani mai gidan burodi, Mutawakil Ahmed Babiker, ya ce farashin fulawa ya ninka, yayin da yawan katsewar wutar lantarki ya tilasta masa kashe kuɗi wajen sayen man fetur don janareta.
Ya yi gargaɗin cewa mai yiwuwa nan ba da jimawa ba zai rufe gidan burodinsa, inda ya ce duk da cewa suna sayar da burodi a farashin da bai kai kuɗin da suke kashewa wajen samar da shi ba, ba za su iya ƙara farashin ba saboda halin ƙunci da jama'a ke ciki.



















