| hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An jinkirta buɗe makarantu a Nijar zuwa 15 ga Oktoba sakamakon ruwan sama
Hukumomi a Nijar sun bayyana cewa jinkirta buɗe makarantu a ƙasar ya zama dole saboda yanayin damina mai tsawo da kuma ambaliya, lamarin da ya sanya makarantu ba sa aiki kana ajujuwa da dama sun cika da ruwa.
An jinkirta buɗe makarantu a Nijar zuwa 15 ga Oktoba sakamakon ruwan sama
Gwamnatin Nijar ta jinkirta lokacin bude makaratu a kasar daga 1 ga Okatoba zuwa 15 ga watan saboda ruwan sama
30 Satumba 2025

Cikin shekaru biyu a jere, tsarin kalandar karatu a Nijar ya fuskanci tsaiko sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da kuma ambaliya da suka tilasta wa gwamnati jinkirta buɗe makarantu a faɗin ƙasar.

A wata sanarwa da ofishin babban sakataren gwamnatin ƙasar ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa an jinkirta shekarar karatu ta 2025-2026 da mako biyu, wato daga ranar 1 ga Oktoba zuwa 15 ga watan Oktoba, kamar yadda jaridar Actu Niger ta rawaito.

Sanarwar wadda babban sakataren Mahamane Roufal Laouali ya sanya wa hannu, ta ce matakin ya shafi ɗalibai kusan miliyan uku a faɗin ƙasar.

Hukumomi a ƙasar sun bayyana cewa, ɗage lokacin buɗe makarantu a Nijar ya zama dole saboda yanayin damina mai tsawo da aka samu, lamarin da ya sanya makarantu ba sa aiki kuma ajujuwa da dama sun cika da ruwa ko kuma suna buƙatar gyara cikin gaggawa.

An umarci gwamanoni da hakimai da jami’an ilimi su haɗa kai domin gyara makarantun gabanin sabuwar ranar da aka sanya ta buɗe makarantu a faɗin ƙasar.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da yanayin damina ke kawo cikas ga tsarin kalandar karatu a Nijar ba. A shekarar 2024, sai da ambaliyar ruwa ta tilasta wa hukumomi jinkirta soma shekarar karatu daga 2 ga watan Oktoba zuwa 28 ga Oktoba.

Hakan ya biyo bayan lalacewar makaratu da dama ko kuma mayar da su wuraren samun mafaka ga iyalai da suka rasa matsugunansu.

Kazalika ɗage lokacin buɗe makarantun ya daɗa ƙara matsin da tsarin ilimin Nijar ke ciki a ƙasar, inda a bana ake sa ran samun ɗalibai kusan miliyan uku.

Adadin ɗaliban dai ya nuna matsalolin da ake fuskanta kamar rashin isassun ajujuwa, da cunkoso a makarantu da kuma ƙarancin malamai.

Rumbun Labarai
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Rubio ya nemi a daina bai wa RSF makamai, ya ɗora wa rundunar laifi kan kashe-kashe a Al Fasher
Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa
Mutum 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana – Rahotanni
Mahaucin Al Fasher: Yadda hotonsa ya zama alamar bakin cikin Sudan
UN Women: Mata da 'yan mata 11M suna fama da matsanancin ƙarancin abinci a Sudan sakamakon yaƙi
WHO ta bayyana damuwa kan karuwar masu ciwon siga a Afirka
Kisan kare dangi a boye da bayyane: Gushewar jinkai a Al Fasher
An ba da belin dan Gaddafi bayan da ya shafe shekaru 10 a tsare a Lebanon
Gwamnatin Trump 'ta aika wa Equatorial Guinea dala miliyan 7.5' don ta karɓi waɗanda Amurka ta kora
Ƙasashe fiye da 20 sun yi Allah wadai da RSF kan kashe-kashen da take yi a Sudan
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi kira da a dakatar da zubar da jini a Sudan
Paul Biya na Kamaru: Dan siyasar da zai ci gaba da yin mulki har sai ya kai shekara 99?
Hare-haren RSF sun kori ƙarin dubban mutane daga Darfur da Kordofan na Sudan
RSF ta binne gawawwaki a kabarin bai-ɗaya, ta ƙone wasu domin 'ɓoye laifukan yaƙi': Likitocin Sudan
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi na RSF a Kordofan ta Arewa
Dakarun Nijar sun cafke muggan makamai da aka yi safararsu daga Libya, sun kama masu safarar ƙwayoyi
RSF ta Sudan ta kai hare-hare a Jihar Khartoum da birnin Atbara bayan amincewa da tsagaita wuta
Paul Biya na Kamaru: Shugaban da ya fi tsufa a duniya ya sha rantsuwar kama aiki karo na takwas
Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata