SIYASA
2 minti karatu
Firaministan Falasɗinu ya bayyana shirin ware dala biliyan 65 don sake gina Gaza
Shirin zaman lafiya na Gaza ya bayar da shawarar a ba da rawar taka wa ga Hukumar Falasdinawa da zarar an gama wasu sauye-sauye.
Firaministan Falasɗinu ya bayyana shirin ware dala biliyan 65 don sake gina Gaza
Firaministan Falasdinu Mustafa ya halarci taro a Ramallah kan shirin sake gina Gaza.
16 Oktoba 2025

Firaministan Gwamnatin Falasdinu ya gana da wakilan Majalisar Dinkin Duniya da jami'an diflomasiyya don gabatar da shirin sake gina Gaza, duk da rashin tabbas kan rawar da gwamnatinsa ke takawa a makomar yankin da yaki ya ruguza.

"Zan so na yi imanin cewa nan da watanni 12, Hukumar Falasdinawa za ta fara aiki gadan-gadan a Gaza," in ji Mohammad Mustafa a ranar Alhamis, kwanaki bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Gaza.

Hukumar Falasdinawa (PA) ba ta da wata rawa a mulkin Gaza tun lokacin da Hamas ta karbe ikon yankin a shekarar 2007, ko da yake har yanzu tana ba da wasu ayyuka a yankin.

Shirin wanzar da zaman lafiya na Gaza da shugaban Amurka Donald Trump ya kawo bai kawar da kafa kasar Falasdinu ba, sannan kuma ya ba da shawarar bayar da damar taka rawa ga Hukumar Falasdinu da zarar ta kammala wasu gyare-gyare.

Mustafa ya ce hukumar ta PA ta tsara wani shiri na shekaru biyar ga Gaza wanda zai gudana a matakai uku, kuma yana bukatar dala biliyan 65 don sassa 18 daban-daban kamar na gidaje, ilimi, gudanarwa da sauransu.

Hadin kan siyasa da kan iyaka

Shirin ya ta'allaka ne kan abin da aka amince da shi a taron kolin kasashen Larabawa a birnin Alkahira a watan Maris din shekarar 2025, kuma Mustafa ya ce "an riga an fara shirye-shiryen horar da 'yan sanda karkashin shirin da aka kulla da Masar da Jordan."

"Manufarmu a bayyane take karara," ya shaida wa taron ministocin Falasdinawa, da shugabannin hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, da shugabannin jami'an diflomasiyya daga ofishinsa da ke Ramallah, a yankin Gabar Yamma da Isra'ila ta mamaye.

"Za a sake gina Gaza a matsayin buɗaɗɗen waje, mai haɗin kai da bunƙasa kuma wani bangare na ƙasar Falasdin," in ji Mustafa.

Ya kuma ce ana ci gaba da tattauna wa ta fasaha tare da Tarayyar Turai kan "amintaccen ayyukan shiga nahiyar, tsarin fito, da rundunonin 'yan sanda na bai daya".

Tarayyar Turai na daga wadanda suka fi bayar da taimako ga Hukumar Falasdin.

Tsarin zai karfafa hadin kan siyasa da yanki tsakanin Gaza da Gabar Yamma, da kuma ba da gudunmawa wajen maido da ingantaccen tsarin gudanar da mulkin kasar Falasdin, in ji Mustafa.

Rumbun Labarai
Kutungwilar Netanyahu kan tsagaita wuta a Gaza ita ce ci gaba da kashe Falasdinawa
Zaben Tanzania: Intanet ya katse sannan zanga-zanga ta barke a ranar zabe
Masu nazarin kayan tarihi sun gano kisan gillar Faransa a wata makabartar Senegal
Mahama ya hana ministoci bayyana manufofin gwamnatin Ghana sai da izinin majalisar ministoci
Shugaban Sudan al Burhan ya ce ‘sojojin ƙasar sun janye’ daga Al Fasher
Hamas na aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta amma Isra'ila na ci gaba da karya ta, in ji Erdogan
Ghana tana alhinin mutuwar matar tsohon shugaban ƙasar, Nana Konadu Agyeman-Rawlings
Kotu a Bangladesh ta tura manyan hafsoshin soji gidan yari a wata shari’a ta tarihi
Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya fara zaman  gidan kaso kan karɓar kuɗin a wurin Gaddafi
Tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga ya mutu a India
Shugaban Madagascar na ɓuya a wani 'wuri mai aminci' bayan mummunar zanga-zangar da ta ɓarke a ƙasar
Yadda diflomasiyyar Erdogan na Turkiyya ta taimaka wajen cim ma tsagaita wuta a Gaza
Burkina Faso ta kama ma’aikatan jinƙai bisa zargin leƙen asiri
Shekaru biyu na kisan kiyashin Isra’ila a Gaza: Yadda Amurka ke kare Netanyahu daga tuhuma
Swahili ne mafita ga Gabashin Afirka ba Faransanci ba
Za a ƙaddamar da shirin bayar da lasisin bindiga na intanet a Ghana
ICC: Yaudara daga wadanda suka kafa ta, mafaka ga mambobin ƙasashen Afirka
Fayyaceccen bayanin Erdogan a MDD: Gaza, 'ƙasar Isra'ila', da makomar yankin
Mene ne daftarin Babban Zauren MDD kan mafitar samar da ƙasashe biyu da ƙarara ya yi watsi da Hamas?
INEC ta buƙaci a hukunta duk wanda ya fara kamfen ɗin 2027 kafin lokaci