Sojin Sudan da dakarun ƙawance sun ƙara matsa gaba a gundumomi uku na Jihar West Kordofan ranar Talata yayin da dakarun rundunar RSF ke ja da baya, kamar yadda majiyoyin soji suka shaida wa Anadolu.
Dakaru sun ƙaddamar da shara a ƙauyuka a faɗin Al-Khuway da wurare da ke arewa da gabashin na Al-Nuhud da Abu Zabad, kamar yadda majiyoyin suka bayyana.
Dar Hamar Emergency Committee, wata ƙungiyar ba da taimakon gaggawa a yankin, ta nemi a ba da abinci da magunguna da abubuwa na buƙatun gaggawa ga Al-Khuway, tana mai cewa sojin ya ƙwace wuraren hukuma a yankin.
Ta kuma yi kira ga hukumomin jihohi da ‘yankasuwa su tura ayarin motoci na kayayyaki zuwa gundumar.
Ƙara samun ci gaba
Mohamed Didan, wani mai magana da yawun dakaru na musamman na sojin ƙasar, ya shaida wa Anadolu ranar Litinin cewa dakarun sun ƙwace Al-Saatat, a arewa maso gabashin Abu Zabad.
Didan ya ce Abu Zabad na haɗa ɓangarorin arewaci da kudancin West Kordofan, lamarin da ya sa yake da muhimmanci sosai.
Ci-gaban ya biyo bayan karɓe iko da Al-Khuway da sojin ya yi ranar Jumma’a ne, kimanin kilomita 100 (mil 62 ) daga Al-Nuhud, in ji jami’an Sudan.
Yaƙin tsakanin sojin ƙasar da rundunar RSF ya ɓarke ne a watan Afrilun shekarar 2023 kuma ya kashe gomman dubban mutane.
Alƙalluma na baya bayan nan na Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majaliusar Ɗinkin Duniya (MƊD) sun ce adadin waɗanda aka tilasta wa barin gidajensu ya kai kimanin mutum miliyan 11.4.




















