| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Ana samun nasara a sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya, amma talauci na ƙaruwa: IMF
Tun bayan hawansa mulki fiye da shekaru uku da suka gabata, Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur wanda ya daɗe yana sa farashin fetur ya yi sauƙi a ƙasar, sannan ya sassauta tsarin canjin kuɗin ƙasar da kuma sake fasalin tsarin haraji.
Ana samun nasara a sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya, amma talauci na ƙaruwa: IMF
IMF ya ƙara da cewa fiye da mutane miliyan 27 sun fuskanci matsalar rashin wadataccen abinci a shekarar. / Reuters

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) a ranar ya ce ce sauye-sauyen da gwamnatin Nijeriya ta aiwatar sun ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar, amma ya yi gargaɗin cewa fiye da kashi 60 cikin 100 na ’yan Nijeriya yanzu suna rayuwa cikin talauci.

Tun bayan hawansa mulki fiye da shekaru uku da suka gabata, Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur mai tsada wanda ya daɗe yana sa farashin fetur ya yi sauƙi a ƙasar, sannan ya sassauta tsarin canjin kuɗin ƙasar da kuma sake fasalin tsarin haraji.

Ko da yake masana tattalin arziki sun ce waɗannan sauye-sauyen sun daɗe suna buƙatar a aiwatar da su, talauci ya ci gaba da ƙaruwa, inda ya shafi kashi 63 cikin 100 na al’ummar ƙasar zuwa ƙarshen shekarar 2025.

IMF ya ƙara da cewa fiye da mutane miliyan 27 sun fuskanci matsalar rashin wadataccen abinci a shekarar.

“A cikin shekaru uku da suka gabata, manyan sauye-sauyen da aka aiwatar sun haifar da ingantattun sakamakon tattalin arziki tare da ƙarfafa juriyar tattalin arzikin ƙasar,” in ji IMF a cikin wata sanarwa bayan nazarinsa na shekara-shekara kan tattalin arzikin Nijeriya.

Sai dai ya ƙara da cewa, “duk da haka, rayuwa tana ci gaba da kasancewa mai wahala ga ’yan Nijeriya da dama.”

Talauci ya shafe shekaru yana ƙaruwa a Nijeriya, ƙasa mafi yawan jama’a a Afirka. A rahotonsa na baya-bayan nan, Bankin Duniya ya bayyana cewa kusan kashi 61 cikin 100 na al’ummar ƙasar suna rayuwa cikin talauci, idan aka kwatanta da kashi 40 cikin 100 a shekarar 2019.

Bankin Duniya ya kuma lura cewa kusan kashi uku cikin huɗu na wannan ƙarin talauci ya faru ne kafin shekarar 2023, lokacin da aka rantsar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa.

 

Rumbun Labarai
Matatar mai ta Dangote ta fara dakon fetur kyauta zuwa wasu jihohin Nijeriya
Majalisar Dattawan Nijeriya ta buƙaci a soke shirin gyaran hali na tubabbun 'yan Boko Haram
Jihar Legas ta kama mabarata 396, tana tantance bayanansu domin mayar da su jihohinsu na asali
Nijeriya za ta binciki manyan kamfanonin fasaha kan amfani da labaran ƙasar ba bisa ƙa’ida ba
Gwamnatin Nijeriya ta bai wa 'yan ƙasarta damar ƙarshe ta kwashe su daga Afirka ta Kudu
‘Yansandan Nijeriya sun dakile harin ‘yanbindiga a Sokoto
Yadda matsalar tsaron Nijeriya ke ƙara barazana ga wadatar abinci
Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da fara ayyukan Bama zuwa Banki da Dikwa zuwa Gamboru-Ngala
Hukumar INEC ta Nijeriya ta tsawaita aikin rajistar masu zaɓe da makwanni biyu
Kotu ta samu mutum biyu da laifin ta'addanci a Nijeriya
Nijeriya ta ƙaddamar da masana'antar sarrafa lithium mafi girma a Yammacin Afirka a jihar Nassarawa
Amurka ta janye akasarin sojojinta da ta aika Nijeriya
Yunwa ta kai mummunan mataki da bai taɓa kai wa ba a shekaru 10 a Arewacin Nijeriya - WFP
Sojojin Nijeriya sun kashe ’yanta’adda 662, sun ceto 951 da aka sace cikin watanni uku
CBN ya soke lasisin ƙananan bankuna na Microfinance 46 saboda rashin cika ƙa’idoji
Nijeriya ta yi alƙawarin tallafa wa 'yan ƙasar 271 da suka dawo daga Afirka ta Kudu
Ɗan Nijeriya ya mutu bayan sakinsa daga kurkuku a Côte d'Ivoire
Gwamnatin Nijeriya ta karɓi 'yan ƙasar 269 da aka sake mayarwa gida daga Afirka ta Kudu
Jam'iyyar adawa ta NDC a Nijeriya ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu game da rajistarta
Sojojin Nijeriya sun ceto ɗalibai da malaman GDSS Lassa 10 a Jihar Borno