Harin RSF a wani asibiti a Sudan ya kashe mutum 22, ciki har da ma'aikatan jinya

Ƙungiyar likitocin Sudan ta zargi dakarun RSF da aikata laifin yaƙi bayan kai harin bam a asibitin soji na Al-Kuweik.

By
Ƙungiyar likitocin ta yi Allaha wadai da harin, tana mai cewa kai hari kan cibiyar jinya da kuma ma’aikatan jinya “laifin yaƙi ne" / Reuters

An kashe aƙalla mutum 22, ciki har da ma’aikatan jinya huɗu, yayin da wasu takwas suka jikkata bayan rundunar RSF ta kai harin bam a asibitin soji na Al-Kuweik a jihar Kudancin Kordofan ta Sudan, kamar yadda wata ƙungiyar ma’aikatan jinya ta bayyana.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, ƙungiyar likitocin Sudan ta ce waɗanda lamarin ya rutsa da su sun haɗa da daraktan asibitin da kuma wasu ma’aikatan jinya uku.

Ƙungiyar ta yi Allaha wadai da harin, tana mai cewa kai hari kan cibiyar jinya da kuma ma’aikatan jinya “laifin yaƙi ne da kuma tsagwaron keta dokokin ƙasa da ƙasa da suka tabbatar da kare fararen-hula da wuraren jinya.”

Ta ce harin wani ɓangare na jerin hare-hare a faɗin jihar Kudancin Kordofan ya tilasta dakatar da ayyuka a wasu asibitoci, lamarin da ya ta’azzara matsalar jinƙai tare da barazana ga abin da ya saura cikin harkar jinya ga fararen-hula.

Ƙungiyar ta ɗoura wa RSF alhakin harin gaɓa ɗaya. Sannan ta yi kira ga ƙasashen duniya da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama su ɗauki mataki nan-take domin kawo ƙarshen hare-hare kan wuraren jinya.

Babu tsokaci nan-take daga RSF game da zargin.

Daga cikin jihohin Sudan18, rundunar RSF tana iko da dukkan jihohi biyar a yankin Yammacin Darfur, face wasu ɓangarori na Arewacin Darfur da kawo yanzu yake ƙarƙashin ikon soji.

Sojin na da iko a yawancin jihohi 13 a faɗin kudanci da arewaci da gabashi da kuma tsakiyar ƙasar, ciki har da babban birnin ƙasar, Khartoum.

Rikicin tsakanin sojin Sudan da ku ma rundunar RSF, wanda ya ɓarke a watan Afrilun 2023, ya kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da gidajensu.