Amurka ta ce akwai yiwuwar kai harin ta'addanci kan ofishin jakadanci da makarantunta a Nijeriya
Ofishin jakadancin Amurka ya shawarci 'yan ƙasar su riƙa sauya hanyoyi da lokutan tafiye-tafiyensu da kuma kauce wa tafiyar da rayuwarsu ta yadda za a iya hasashen abin da za su yi nan gaba tare da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana.
Gwamnatin Amurka ta fitar da gargaɗi na yiwuwar kai harin ta’addanci kan ofisoshin jakadanci da makarantun da ke alaƙa da ita a Nijeriya.
A wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka ya fitar a Abuja ranar Litinin, ya bai wa ‘yan ƙasar Amurka shawara su ɗauki ƙarin matakan tsaro idan za su ziyarci harabar ofisoshin jakadancin Amurka da kuma makarantu da ke da alaƙa da Amurka.
Gargaɗin ya ambato ofisoshin jakadancin Amurka a Abuja da Legas inda ya yi kira ga Amurkawa su sanya ido sosai kuma su ɗauki ƙarin matakan tsaro yayin zuwa waɗannan wuraren.
Ofishin jakadancin ya ce ya kamata ‘yan ƙasar su yi ta sauya hanyoyi da lokutan kai-komonsu da kuma kauce wa yanayin da za a iya yin hasashen yadda suke gudanar da lamuransu tare da mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa kusa da su domin rage barazanar da za ta iya tasowa.
“Dole ‘yan Amurka su ɗauki ƙarin matakan rigakafi yayin tafiya zuwa ofishin jakadancin Amurka da ƙaramin ofishin jakadanci da ke Legas da kuma makarantu masu alaƙa da Amurka,” in ji sanarwar.
Shawarar ta nemi Amurkawa su rage fita daban cikin jama’a da kuma kauce wa cunkoson jama’a da zanga-zanga tare da sanar da ‘yan’uwansu tsare-tsaren tsaronsu.
Sauran shawarwarin sun haɗa da tabbatar da cewa wayoyin salularsu na da cikakken caji domin ko-ta-kwana da kuma sanin hanyoyin ficewa cikin gaggawa kafin su shiga ko wane gini.
Duk da gargaɗin, ɓangaren jakadanci na ofisoshin jakadancin Amurka a Abuja da Legas za su ci gab da aiki, in ji sanarwar.
Ofishin ya buƙaci ‘yan Amurka a Nijeriya su ci gaba da bibiyar adireshin ofishin jakadancin na intanet domin ƙarin bayani tare da bin shawarwarin ma’aikatar harkokin wajen Amurka.
Gargaɗin na zuwa ne yayin da ake yaƙi tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran bayan Amurka da Isra’ila sun kai hari Iran inda aka kashe jagoran addinin ƙasar Ali Khamenei.