Isra'ila na karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, ta ci gaba da kai hari

A harin baya bayan da ta kai, Isra'ila ta ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta a kudancin Lebanon inda ta kashe mutum guda da jikkata wasu mutanen biyu.

By
Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a kudancin Lebanon duk da yarjejeniyar tsagaita wuta. / AA

Isra’ila ta kashe mutum guda da jikkata wasu biyu a hari ta sama a kudancin Lebanon, wanda hakan ne karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta baya bayan da ta yi wadda aka cim ma tun Nuwamban 2024.

Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta ce an kai harin ranar Litinin a garin Tyre.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce Cibiyar Ayyukan Lafiya na Gaggawa ta bayyana mutuwar mutum daya da jikkatar wasu biyu sakamakon harin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa na Lebanon (NNA) ya rawaito cewa wani jirgi marar matuki na Isra’ila ya doki wata mota a wajen garin Tyre.

Sanarwar ta kuma ce wasu jiragen marasa matuka na Isra’ila na shawagi a sararin samaniyar yankunan Zahrani da Bisariyeh da ke kudancin Lebanon, inda wani jirgin ya jefa bam mai kara a kan wani kamfanin samar da marble da ke kan hanyar Adissa-Markaba.

Daga baya kungiyar Hezbollah ta sanar da cewa harin na Tyre ya kashe dan jaridar gidan talabijin na Al manar, Ali Nour Al Din bayan an hari motarsa.

A wata sanarwa da ta fitar ta daban, Hezbolla ta yi gargadi kan hatsarin yadda makoya ke ci gaba da kai hari ciki har da ma kan kafafen watsa labarai.

“Muna suka da babbar murya kan kisan gilla da makiyiya Isra’ila ta yi wa dan jarida Nour al-Din,” in ji sanarwar.

A wani rahoton na daban, NNA ya rawaito cewa wata tankar Isra’ila ta hari wani gida a wajen garin Aitaroun a gundumar Bint Jbeil da ke kudancin Lebanon.

Kazalika kamfanin ya rawaito cewa an kai harin bama-bamai kan gidaje a yankin Hreika da ke wajen garin Aitaroun, kuma an kai hare-haren daga sabon sansanin soji da Isra’ila ta kama a Jabal Al-Bat.

Isra’ila ta kashe daruruwan ‘yan Lebanon yayin karya yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma tana ci gaba da mamayar kudancin Lebanon.

A watan Oktoban 2023 ne Isra’ila ta fara kai hare-hare Lebanon inda a watan Satumban 2024 ta mayar da lamarin cikakken yaki tare da kashe sama da mutane 4,000.