| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
Manoma biyar sun rasu bayan kwale-kwale ya kife a Jihar Neja ta Nijeriya
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Shaba-Woshi-Kpaya, da ke gundumar Edotsu a lokacin da manoman ke kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu.
Manoma biyar sun rasu bayan kwale-kwale ya kife a Jihar Neja ta Nijeriya
Hadarin kwale-kwale ya zama ruwan dare a al’ummomin da ke zaune a bakin koguna a Nijeriya

Manoma biyar, maza huɗu da mace ɗaya, sun mutu bayan wani kwale-kwale ya kife a Kogin Kudi, a Ƙaramar Hukumar Katcha ta Jihar Neja da ke arewacin Nijeriya.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a ƙauyen Shaba-Woshi-Kpaya, da ke gundumar Edotsu, a cewar ganau.

Wani mazaunin yankin, Muhammadu Dan-Asabe, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa mutanen suna kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu ne lokacin da kwale-kwalen ya kife.

Daraktan Yaɗa Labarai da Ayyuka na Musamman na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dr Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce waɗanda abin ya rutsa da su suna tafiya ne daga ƙauyensu zuwa gonakinsu lokacin da kwale-kwalen ya kife.

An bayyana sunayen mamatan da Yahaya Abubakar, Usman Abubakar, Lami Hussaini, Baba Ahmadu da Salihu Aliyu.

Hussaini ya ce an gano gawawwakin mutanen biyar kuma an yi musu jana’iza a ranar Asabar.

Hadarin kwale-kwale ya zama ruwan dare a al’ummomin da ke zaune a bakin koguna, musamman a lokacin damina da noman rani, lokacin da mazauna yankunan ke dogaro da hanyoyin ruwa domin zuwa gonakinsu.

 

Rumbun Labarai
INEC ta ayyana Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Osun
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga 'yan Nijeriya da ke ketare su zuba jari a Nijeriya
Tinubu ya yi alƙawarin farfaɗo da matatun man Nijeriya da suka jima ba sa aiki yadda ya kamata
Shugabannin addinai a Nijeriya sun sa hannu kan yarjejeniyar inganta zaman lafiya da fahimtar juna
An gano gawawwaki 9 a Jihar Neja ta Nijeriya, kwanaki bayan ceto mutane 308 da aka yi garkuwa da su
Kaduna, Sokoto, Zamfara da wasu jihohin Nijeriya 10 na fuskantar barazanar ambaliya - NiMet
‘Yansandan Nijeriya 10 sun rasa rayukansu a musayar wuta da mahara a arewacin ƙasar, in ji hukumomi
'Yan Nijeriya sun kashe Naira tiriliyan 6.6 kan sayen datar waya a cikin shekara ɗaya
Mutane 237 ne suka mutu sakamakon zazzaɓin Lassa a watanni bakwai na 2026 a Nijeriya - NCDC
Sojojin Nijeriya sun kashe Abu Khalid Al Muhajir da wasu  kwamandojin ISWAP tara a Borno
Masarautar Kano ta musanta bidiyon da ake yadawa kan Sarki Sanusi II ya samu 'carry-over' a jami'a
Super Falcons da Indomitable Lionesses na gogayyar shiga Gasar Kofin Duniya
Gwamnatin Nijeriya za ta fara sarrafa kayayyakin tsara iyali a cikin ƙasar
Hukumar EFCC ta rufe asusun gwamnatin Jihar Osun kwanaki kaɗan kafin zaɓen gwamna
Rundunar sojin Nijeriya ta sanya tukuicin N60m kan kwamandan ISWAP da mataimakinsa
An yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja
An saki gomman mutanen da aka yi garkuwa da su a Jihar Kwara bayan wata shida a hannun ‘yanta'adda
WAEC ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 167,486
Dakarun Nijeriya sun kama mutanen da ake zargi da kai wa  'yan Boko Haram ƙwayoyi a Borno da Yobe
Gwamnati ta ba jami’o’i da kwalejojin Nijeriya umarnin korar ɗalibai da ke da alaka da satar mutane