Wasu fasinjoji sun jikkata a hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna

Babban daraktan hukumar layin dogo na Nijeriya, Kayode Opeifa ya tabbatar da aukuwar lamarin ga kafafen watsa labaran ƙasar inda ya tabbatar da cewa ba a rasa rai ba a hatsarin.

By
Hatsarin jirgin kasa / Others

Hukumar da ke kula da layin dogo ta Nijeriya (NRC) ta tabbatar da cewa wasu fasinjoji sun ji rauni bayan wani hatsari kusa da tashar jirgin ƙasa ta Asham a layin dogon Abuja zuwa Kaduna da safiyar Litinin.

A wata sanarwar da hukumar ta fitar, babban daraktan hukumar NRC Kayode Opeifa ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe kuma ya shafi wani bangaren jirgi ne da ya bugi wanda ke gabansa, kamar yadda kafar talabijin ta Channels ta ƙasar ta ruwaito.

Opeifa ya tattabar da cewa nan take aka garzaya da fasinjojin da suka ji raunin asibitin da ke kusa domin kula da su yayin da ya ƙara da cewa ba a rasa rai ba a hatsarin.

Darakatan na hukumar NRC ya kuma bayyana cewa nan take aka tayar da matakan agajin gaggawa kuma aka tura ma’aikata masu ruwa da tsaki inda lamarin ya auku.

Ya bayyana cewa cibiyar bincike kan kariya ma tana inda lamarin ya auku domin gudanar da bincike kan hatsarin kamar yadda tsare-tsaren kariya ya tanada.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa daga bisani jirgin ya kai ga tashar jirgin ƙasa na Idu da misalin ƙarfe 10:39 a.m., inda ya yi lattin minti 38, bayan an cire ɓangaren da lamarin ya shafa daga jirgin.

Hukumar ta layin dogon Nijeriya ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ta fi mayar da hankali ne kan amincin masu hawa jiragen ƙasan kuma tana ɗaukar dukkan matakai da ya suka kamata domin magance matsalar.