| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Tinubu ya ba da umarnin fitar da kudi nan-take don gyara kayan aikin sararin samaniyar Nijeriya
Ya jaddada jajircewar gwamnatinsa wajen cim ma manufa da tsarin sararin samaniyar Nijeriya kamar yadda aka gabatar a cikin sabon shiri na shekara 25 na inganta tsarin sararin samaniyar ƙasar.
Tinubu ya ba da umarnin fitar da kudi nan-take don gyara kayan aikin sararin samaniyar Nijeriya
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu / Reuters
awa ɗaya baya

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin fitar da kudi nan-take domin gyara kayayyakin aikin sararin samaniyar Nijeriya bisa tsarin da aka shimfiɗa na inganta sararin samaniyar ƙasar.

Ya jaddada jajircewar gwamnatinsa wajen cim ma manufa da tsarin sararin samaniyar Nijeriya kamar yadda aka gabatar a cikin sabon shiri na shekara 25 na inganta tsarin sararin samaniyar ƙasar.

“Na amince yanzu a turo adadin kuɗin da ake buƙata ga majalisar zartarwar tarayya domin ta yi nazari sannan ta amince da aiwatar da tsarin shekara 25 na manufar sararin samaniyar Nijeriya,” in ji shi.

Shugaba Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya wakilta, ya ba da umarnin ne ranar Talata a lokacin taron Hukumar Sararin Samaniyar Ƙasar na farko da aka yi a fadar shugaban ƙasar a Abuja.

Ya ce , “Nijeriya ba za ta zama ‘yar kallo ba kawai yayin da sabon ɓangaren ci-gaba ke bunƙasa. Za mu shiga ciki, za mu yi gogayya, za mu ba da tamu gudunmawar. Dole mu tsara shirinmu na sararin samaniya bisa fayyace gaskiya da muradun ƙasa.

“Dole mu gina wani tsari da zai yi hidima ga manomi a gona da malami a aji da mai bincike a ɗakin bincike da ɗankasuwa a kasuwa da soja a kan aiki da kuma mai tsara manufofi wanda dole ya yi tsare-tsare bisa hujja maimakon zato kawai. Ta haka ne ƙasa ke sauyawa domin samun fa’ida.”

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa, a manufarta ta sabunta fata, ta mayar da hanlaki kan ciyar da al’ummar gaba “ta hanyar amfani da arzikin jama’arta wajen inganta tattalin arziki da al’ummar ƙasar.

“Za mu jajirce domin ba da tallafin da ake buƙata wajen nasarar tsarin sararin samaniyar tare da ababen da ake buƙata wajen bunƙasa shi da kuma nasarar cim ma manufar hukumar sararin samaniya ta ƙasa,” in ji shi.

Shugaban ya bayyana cewa jarin da gwamnatinsa ke zubawa a fannin na zuwa ne bisa damarmakin da ke fannin sararin samaniya “a matsayin wani sabon ɓangare na ci gaban bil’adama, a matsayin wani abin ƙara kuzari na ƙarin inganta fasaha da kuma faɗaɗa harkokin tattalin arziƙi.”

Ya bayyana cewa sararin samaniya na ba da “wani ƙalubale na daban da kuma wata kafa ta bincike mai tasiri da kuma samun ma’aidinai tare da kare muhalli.

Shugaba Tinubu ya ci gaba da cewa: “Kawo yanzu fasahar sararin samaniya ita ce ginshiƙin tsaron intanet da kuma ingantaccen tattalin ariki na intanet. Tattalin arzikin sararin samaniya na haɓaka cikin sauri kuma ana sa rai zai zarce dala tiliriliyon ɗaya nan da shekarar 2040. Idan muka zuba jari a sararin samaniya, ba za mu daɗe ba za mu samu sakamako mai kyau.”

Ya ƙara da cewa, “Muna saka kudi ne kan harkar noma mara kuskure da tsaro a kan iyakokinmu; muna saka kuɗi ne kan tsare-tsaren ba da gargaɗi da wurwuri game da ambaliyar ruwa da gobara da birane da suka fi kafin basira da sararin samaniya mai ƙarin tsaro da ingantacciyar sadarwa da kuma tattalin arzikin intane da zai iya gogayya da mafi girma a duniya. Muna ba da kuɗi ga ƙwarin gwiwar wata ƙasa da ta ƙi ta maƙale a takunkumin jiya.”