| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Raul Gonzalez ya zama kocin ƙwararru a karon farko, ya karɓi ragamar Real Oviedo ta Sifaniya
Wannan ne karon farko da Raul zai horar da wata babbar ƙungiya, bayan ya shafe shekaru yana jagoranta ƙananan tawagogin makaranta ƙwallo ta Real Madrid.
Raul Gonzalez ya zama kocin ƙwararru a karon farko, ya karɓi ragamar Real Oviedo ta Sifaniya
Raul Gonzalez na da shekaru 49 a duniya

Tsohon ɗanwasan Real Madrid kuma tsohon kyaftin ɗin tawagar Sifaniya, Raul Gonzalez ya karɓi ragamar babbar ƙungiya a karon farko na rayuwarsa ta kocin ƙwallon ƙafa.

Mai shekaru 49, Raul ya zama kocin Real Oviedo ta Sifaniya, kuma zai fara jagorantar wasan farko tare da ƙungiyar ranar Asabar 14 ga Nuwamban 2026, inda za su kara da Girona a gasar La Liga 2.

Real Oviedo ta naɗa Raul ya zama sabon kocin babbar tawagarta, inda ya maye gurbin Julian Calero, wanda aka sallama duk da ba a daɗewa.

Wata sanarwa daga ƙungiyar ta tabbatar da sanya hannu kan kwantiragi da Raul, wadda za ta kai zuwa 30 ga Yunin 2028. Zai fara nan-take don kammala kakar bana da ba ta yi nisa ba.

Wannan ne karon farko da Raul zai horar da wata babbar ƙungiya, bayan ya shafe shekaru yana jagoranta ƙananan tawagogin makaranta ƙwallo ta Real Madrid tun daga 2018.

Lokacin da ya ja ragamar ƙungiyar Real Madrid Castilla tsawon kaka shida, tun daga 2018, kuma ya lashe kofin matasa na UEFA Youth League a 2020.

Raul Gonzalez ɗaya ne cikin mashahuran taurari a tarihin ƙungiyar Real Madrid, wanda ya kwashe shekaru 15 a can.

Ya lashe kofunan La Liga 6 da na Zakarun Turai 3, da UEFA Supercup 1, kuma sau 3 yana zama gwarzon ɗanwasan gaba na shekar na UEFA Club, baya ga sauran kofunan da ya ci a wasu ƙungiyoyi.