'Yan Habasha sun isa rumfunan zabe da wuri a ranar Litinin, inda aka yi hasashen Jam'iyyar PP ta Firaiminista mai ci Abiy Ahmed za ta yi nasara da rinjaye, a cewar masu sharhi.
Tun daga shekarar 2018 Abiy ya ke rike da mulki a ƙasar da ke yankin kusurwar Afirka mai mutane miliyan 130. A shekarar 2019, ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel saboda gyara dangantaka da makwabciyar ƙasar Eritrea.
An yi ta samun dogayen layuka a rumfunan zaɓe a babban birnin kasar Addis Ababa, kamar yadda wakilan kamfanin dillancin labaran AFP suka ga wasu masu kada kuri’a sun kawo kujera don rage jira.
"Lokaci ne mai matukar muhimmanci da za a yanke hukunci kan makomar kasarmu," in ji Binyam Gideyelem, mai shekaru 38, ma'aikacin hukumar sadarwa wanda ya fito kaɗa kuri'a a karon farko, a wani tasha kusa da babban filin jirgin sama na kasa da kasa.
"Ina so na yi amfani da 'yancina a matsayina na ɗan kasa," in ji Seife Desta mai shekaru 77.
Babu hamayya daga Jam'iyyun adawa
Da ‘‘alama zaɓen zai zama ɗaya daga cikin manyan zaɓuka bakwai da aka yi a kasar da babu adawa sosai tun bayan gabatar da tsarin dimokuraɗiyya na jam'iyyu da yawa a shekarar 1991,’’ kamar yadda masu nazari daga Charham House Ahmed Soliman da Abel Abate Demissie suka wallafa a makon da ya wuce.
Jam'iyyar PP ta Abiy ta lashe kashi 96 cikin 100 na kujerun a zaɓen da ya gabata a shekarar 2021.
'Yan adawa suna takara da ƙarancin albarkatun kuɗi kana sun rabe cikin jam'iyyu fiye da 40. A cikin gundumomi da dama, jam'iyyar mai mulki tana takara ba tare da hamayya ba.
Masu adawa da jam’iyyar PP mai mulki da dama ba za su iya fafatawa a zaɓen ba,’’ in ji Chatham House. ‘‘Wasu suna gudun hijira, wasu kuma an haramta musu [shiga zaɓen], yayin da wasu suke ɗaure, haka kuma da yawa ba su samu abin da zai karfafa musu gwiwar yin gwagwarmaya da gwamnatin mai ci ba.’’
Tun da misalin ƙarfe 6:00 na safe (03:00 agogon GMT) aka buɗe rumfunan zaɓe kuma ana sa ran rufe su da misalin ƙrfe 6:00 na yamma, inda ake da mutane fiye da miliyan 50 da suka cancanci kaɗa ƙuri'a a faɗin rumfunan zaɓe 48,000 a babban birnin.
Ana sa ran fitar da sakamako a cikin kwanaki 10 bayan rufe rumfunan kaɗa kuri’un zaɓe.
Rikice-rikicen makamai
Babu wani zaɓe da ake gudanarwa a yankin arewacin Tigray, saboda tashe-tashen hankula da ake ci gaba da fuskanta tsakanin hukumomin yanki da na tarayya.
Fiye da mutane miliyan ɗaya ne suka rasa matsugunansu saboda mummunan yakin basasar shekarar 2020-2022.
Duk da waɗannan ƙalubalen, tattalin arzikin Habasha na ƙaruwa a ɗaya daga cikin matakai mafi sauri a duniya - kuma ana sa ran zai wuce kashi tara cikin ɗari a wannan shekarar, a cewar Asusun Ba da Lamuni na Duniya.
Nasarar hakan ta biyo bayan irin kayayyakin more rayuwa da jarin masana’antu ƙarkashin gwamnatocin da suka gabata suka yi, ko da yake sauye-sauyen baya-bayan nan ƙarkashin Abiy sun taimaka wajen haɓaka fitar da kayayyaki duk da wahalar ɗan wani lokaci da ‘yan ƙasar suka fuskanta.
Babu wata alama ta rage rikice-rikice a jihohi biyu mafi yawan jama'a, Oromia da Amhara.
A Amhara, mai yawan jama'a kusan miliyan 20, 'yan tawayen Fano na ƙasa sun yi barazanar kawo cikas ga tsarin zaɓe, ko da yake Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta soke zaɓe a mazabu takwas kacal daga cikin mazabu 137 da ke jihar.
Hukumar ta dage cewa za a bude rumfunan zabe a duk fadin yankin Oromia, wanda ya ƙunshi kashi daya bisa uku na girman kasar, inda 'yan tawayen Oromia Liberation Army ke aiki tun daga shekarar 2018.
Masu sa ido kan zaɓen daga kungiyar Tarayyar Afirka, wacce hedikwatarta ke Addis Ababa, da kuma kungiyar yankin Gabashin Afirka IGAD, sun mayar da hankali kan zaɓen da ya kankama a ranar Litinin.
Habasha ba ta amince da shawarar da Tarayyar Turai ta bayar na aika da masu sa ido kan zaɓen ba, a cewar wata majiyar EU.













