| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Akwai ramukan haƙar ma'adinai fiye da 4,000 da aka yi watsi da su a Filato — Alake
Ministan ya bayyana wannan ne a wata sanarwar da mai taimaka masa ta musamman kan watsa labarai, Lara Owoeye-Wise ta fitar ranar Lahadi bayan mutuwar mutum bakwai a ruftawar wata mahaƙar ma'adinai a Kassa, Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta jihar Filato.
Akwai ramukan haƙar ma'adinai fiye da 4,000 da aka yi watsi da su a Filato — Alake
Ministan ma'adinai na Nijeriya Dele Alake

Ministan Harkokin Ma’adinai na Nijeriya, Dele Alake, ya gargaɗi masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba su “daina kashe kansu” ta hanyar haƙar ma’adinai daga ramukan da aka yi watsi da su ba tare da lasisi.

Alake ya ce, akwai ramukan haƙar ma’adinai fiye da 4,000 da aka yi watsi da su a jihar Filato.

Ministan ya bayyana wannan a wata sanarwar da mai taimaka masa ta musamman kan harkar watsa labarai, Lara Owoeye-Wise, ta fitar bayan mutuwar mutum bakwai a wata ruftawar mahaƙar ma’adinai a Kassa, Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta jihar Filato.

Alake ya yi kira ga masu zuba jari su haɗa-kai da gwamnati domin sake sarrafa irin waɗannan mahaƙar ma’adanan domin yin ayyuka masu riba.

Da yake mayar da martani kan ruftawar wata mahaƙar kuza da aka yi watsi da ita, ministan ya ce da za a iya kaucewa rashin, da a ce masu haƙar ma’aidanai ba bisa ƙa’ida ba sun haɗa wata ƙungiyar taimakon kai-da-kai, kuma sun nemi lasisi daga gwamnati.

Gyaran mahaƙa

Alake ya ce da lasisi zai iya ba su damar cin moriyar horarwa ta ɓangaren horar da ƙananan masu haƙar ma’adinai na ma’aikatar, tare da tabbatar da samun kuɗaɗen shiga akai-akai.

Yayin da yake kira ga ƙananan masu haƙar ma’adinai a faɗin ƙasar su koyi darasi daga baƙin cikin da ruftawar mahaƙar ma’adanan ta haddasa a ƙasar, ministan ya yi wa mutane da gwamnatin jihar Filato jaje game da aukuwar lamarin tare da addu’ar Allah ya jiƙan mamatan.

“Ƙalubalen da ke gaban gwamnatin jihar da ta tarayya shi ne yadda za a mayar da waɗannan mahaƙar mutuwar zuwa cibiyoyi na wadata na murna”, a cewar Alake.

Ya ce gwannati na maraba da masu zuba jari wajen sake sarrafa waɗannan mahaƙar ma’adanan domin ayyuka na makamashi da yawon buɗe-ido da kuma kiwon kifi.

Alake ya ce haɗa kai da ‘yankasuwa ita ce hanyar da ta fi sauri wajen mayar da matattun kadarorin ababen da za su yi amfani, yana mai ƙarawa da cewa ma’aikatar ta gyara wuraren haƙar ma’adinai 59 da aka yi watsi da su kawo yanzu.

Rumbun Labarai
Tinubu ya ceci Nijeriya daga wargajewa, in ji Kashim Shettima
Yawan iskar gas ɗin da Nijeriya ke samarwa a cikin gida ya ɗara ƙafa biliyan 2
Mutfwang ya gana da Tinubu, ya ce an fara gurfanar da masu kai hare-hare a Filato
'Yansandan Nijeriya sun ceto mutane 10 daga cikin 'yan NYSC da aka yi garkuwa da su a jihar Imo
Nijeriya: Mutane uku sun mutu a turmutsitsin rabon tallafin kuɗi a Jihar Neja
Ranar 'Yancin Kai a Nijeriya: Sauye-sauyen da muke yi za su haifar da sakamako mai kyau - Tinubu
Dubban fasinjojin Kano da suka bi Saudi Airline sun koka cewa kayansu sun maƙale a Saudiyya
Rundunar Sojin Nijeriya ta ƙaddamar da motocin yaƙi masu sulke da bataliyar soji uku a jihar Kebbi
'Yansandan Nijeriya sun gano ƙoƙon kawuna 28 a wani daji a Jihar Abia
Kotun Nijeriya ta umarci NMDPRA ta bai wa A.A Rano, AYM Shafa da Matrix lasisin shigo da fetur
An sace fiye da mutum 80 a cikin mako biyu a arewacin Nijeriya
‘Yan Nijeriya fiye da 67,000 sun amfana da shirin ba da lamuni ga ƙananan masana'antu – Tinubu
Tinubu yana nan lafiya, zai koma Nijeriya a makon nan: Fadar Shugaban ƙasa
Kwalara ta kashe wasu fursunoni a gidan gyaran hali na Kurmawa da ke Kano
Sojojin Nijeriya sun kama mutum uku da ake zargi da yi wa ‘yanta’adda aikin masinja a Katsina
An sake harbe wani ɗan Nijeriya har lahira a Afirka ta Kudu
Nijeriya ta buƙaci a bai wa Afirka kujeru biyu na dindindin a Kwamitin Tsaro na MƊD
Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar biliyan $700 a ɓangaren haƙar ma'adinai
Ƙungiyar Amnesty International ta soki gwamnatin jihar Kano a Nijeriya kan musguna wa ‘yan adawa
Ba na da-na-sanin taimaka wa waɗanda suka yi watsi da ni a yanzu— El-Rufai