| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
An yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja
Hukumar Binciken Yanayin Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) ta ce ofishinta da ke Utako ya ba da rahoton jin motsin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe a ranar Talata, lamarin ya auku daga nisan kilomita ɗaya ta ƙasa.
An yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja
An ji motsin ƙasa a wasu yankuna na babban birnin tarrayar Nijeriya a Abuja

Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da cewa an yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja, babban birnin tarayyar ƙasar a ranar Talata.

Ministan Ma’adinai na ƙasar Dele Alake ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Lara Owoeye-Wise ta fitar ranar Laraba.

Hukumar Binciken Yanayin Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) ta ce ofishinta da ke yankin Utako ya ba da rahoton jin motsin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe a ranar Talata.

Hukumar ta ce lamarin ya auku ne a yanki mai nisan kilomita ɗaya ta ƙasa kuma ya yi tafiyar kilomita huɗu cikin daƙiƙa biyar.

A cewar NGSA, motsin ƙasar ya kai ƙarfin maki 1 zuwa 2 a ma'aunin Mercalli, inda ta bayyana yanayin da mai sauƙi da ba zai iya haifar da lalacewar gine-gine ko barazana ga rayuka da dukiyoyi ba.

Sanarwar ministan ta ce tuni aka ɗauki matakan gaggawa na gudanar da bincike domin tabbatar da tsaron lafiya da kadarorin mazauna birnin.

Kazalika Dele Alake ya umarci hukumar NGSA da ta samar da sabbin bayanai a-kai-a-kai game da yanayin domin ci gaba da tantance ainihin abi da ya faru da kuma yiwuwar yin aiki tare da sauran hukumomin gwamnati.

Ministan ya yi kira ga mazauna birnin da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullun ba tare da wata damuwa ba

Duk da cewa Nijeriya ba ta cikin manyan yankunan da ake samun iftila’in girgizar ƙasa a duniya, amma ana samun motsin ƙasa mara ƙarfi a wasu lokutan a Abuja da wasu jihohi, wanda hakan ke nuna buƙatar ci gaba da sa ido kan yiwuwar aukuwar girgizar ƙasa da kuma shirye-shiryen gaggawa.

 

Rumbun Labarai
Majalisar Wakilan Nijeriya ta aika da ƙudirin kafa ’yansandan jihohi ga majalisun dokokin jihohi
Rikicin Amurka da Iran: NLC ta nemi gwamnatin Nijeriya ta ɗauki mataki bayan litar mai ta kai N1,500
Dakarun Nijeriya sun kubutar da mutane 31 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Kebbi
Rundunar sojin Nijeriya 'ta kashe ‘yanta’addan Boko Haram da ISWAP fiye da 1000 a shekara ɗaya'
Samun ɗa namiji magaji ba ya gabana - Aliko Dangote
Rundunar 'yansandan Nijeriya ta yi gargaɗi game da yiwuwar kai hare-hare makarantu da wuraren ibada
Ana zargin ‘yanta’adda da kashe aƙalla mutum 13 a wasu hare-hare a Jihar Filato ta Nijeriya
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum 262, sun kuma ceto 27 da aka yi garkuwa da su
An sace malamai shida da suka je taron addu’ar APC a Zamfara
Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah wadai da kisan 'yan ƙasarta biyu a Afirka ta Kudu
FBI ta nemi haɗin kan EFCC don gudanar da bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗen tallafin Amurka
Majalisar Dokokin Nijeriya ta dakatar da ziyarar aiki zuwa Afirka ta Kudu
Tinubu ya bai wa kowace 'yar tawagar ƙwallon kwandon Nijeriya dala dubu ɗari-ɗari
Mutum 511 sun kamu da cutar mashaƙo a Jihar Yobe a Nijeriya
Amurka ta aika sabbin kayayyakin soji Nijeriya
Zaben Nijeriya na 2027: Matakan Tinubu na rage talauci da alƙawarin Atiku na mayar da tallafin fetur
Jakadan Nijeriya ya ziyarci ’yan kasar 198 da ke gidan yari a Indiya
Mutane da dama sun mutu yayin da wasu ke asibiti bayan sun sha wani maganin gargajiya a jihar Ondo
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta kama wasu mutane da kudade da ake zargin kuɗin fansa ne
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum biyu kan zargin kashe Danshagamu a Kano