| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
An yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja
Hukumar Binciken Yanayin Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) ta ce ofishinta da ke Utako ya ba da rahoton jin motsin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe a ranar Talata, lamarin ya auku daga nisan kilomita ɗaya ta ƙasa.
An yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja
An ji motsin ƙasa a wasu yankuna na babban birnin tarrayar Nijeriya a Abuja

Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da cewa an yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja, babban birnin tarayyar ƙasar a ranar Talata.

Ministan Ma’adinai na ƙasar Dele Alake ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Lara Owoeye-Wise ta fitar ranar Laraba.

Hukumar Binciken Yanayin Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) ta ce ofishinta da ke yankin Utako ya ba da rahoton jin motsin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe a ranar Talata.

Hukumar ta ce lamarin ya auku ne a yanki mai nisan kilomita ɗaya ta ƙasa kuma ya yi tafiyar kilomita huɗu cikin daƙiƙa biyar.

A cewar NGSA, motsin ƙasar ya kai ƙarfin maki 1 zuwa 2 a ma'aunin Mercalli, inda ta bayyana yanayin da mai sauƙi da ba zai iya haifar da lalacewar gine-gine ko barazana ga rayuka da dukiyoyi ba.

Sanarwar ministan ta ce tuni aka ɗauki matakan gaggawa na gudanar da bincike domin tabbatar da tsaron lafiya da kadarorin mazauna birnin.

Kazalika Dele Alake ya umarci hukumar NGSA da ta samar da sabbin bayanai a-kai-a-kai game da yanayin domin ci gaba da tantance ainihin abi da ya faru da kuma yiwuwar yin aiki tare da sauran hukumomin gwamnati.

Ministan ya yi kira ga mazauna birnin da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullun ba tare da wata damuwa ba

Duk da cewa Nijeriya ba ta cikin manyan yankunan da ake samun iftila’in girgizar ƙasa a duniya, amma ana samun motsin ƙasa mara ƙarfi a wasu lokutan a Abuja da wasu jihohi, wanda hakan ke nuna buƙatar ci gaba da sa ido kan yiwuwar aukuwar girgizar ƙasa da kuma shirye-shiryen gaggawa.

 

Rumbun Labarai
Darakta Janar na DSS ya umarci jami'ansu da kar su kama kowa yayin da farar-hula suka samu sabani
Nijeriya ta musanta zargin goyon bayan yunƙurin 'juyin mulki' a Nijar
Hukumar DSS ta Nijeriya ta ƙwato bindigogi 676 da harsasai 332,000
INEC za ta yi zaɓen gwaji na Shugaban Ƙasa gabannin zaɓen 2027 na Nijeriya
Ɓarayin daji sun ƙaƙaba harajin naira miliyan 40 kan mazauna wani gari a Sokoto
An lalata makarantu fiye da 1000, an kashe malamai 2,295 a Arewa maso Gabashin Nijeriya - Hukumomi
Annobar da ake zargi mashaƙo ce ta kashe aƙalla mutum 23 a Jihar Filaton Nijeriya
Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da kashe ‘yanta'adda 1,500 da kubutar da mutane 777 a watanni biyu
EFCC ta kori ma’aikatanta fiye da 40 saboda zargin cin hanci da rashawa a Nijeriya
Tinubu ya jinjina wa jami’an tsaron Nijeriya kan ceto masu yi wa kasa hidima da aka yi garkuwa da su
Gwamnatin Kano tana bukatar rigakafin cutar mashaƙo miliyan tara daga gwamnatin tarayya
Nijeriya ta nuna damuwa kan abin da ya faru a makwabciyarta Nijar
Shugaba Tinubu zai tafi Turai don fara hutun makonni uku
Babban Sufeton ‘Yansandan Nijeriya ya matsa ƙaimi don ceto waɗanda aka sace a masallacin Jihar Neja
'Yansandan Nijeriya sun kama likitoci kan zargin safarar mutane da cire musu ƙoda
Amurka na shirin janye sojojinta 200 da ta tura Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta gargaɗi al’ummomi 915 a jihohi 19 kan barazanar ambaliyar ruwa
Sufeta Janar na ’Yansandan Nijeriya ya tura AIG zuwa jihar Neja don ceto masallatan da aka sace
EFCC za ta ba da ladan kashi 5 cikin 100 ga wanda ya ba da bayanai kan kadarorin sata da ke ƙetare
Hedikwatar tsaron Nijeriya ta tattauna da jakadan Saudiyya kan ƙarfafa alaƙar tsaro