Wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.8 ta afka wa kudancin Philippines a ranar Litinin, inda ta kashe aƙalla mutum takwas, in ji hukumar ba da agaji gaggawa ta ƙasar.
Girgizar ƙasar ta sa gine-gine sun rufta kuma ta sa an fara gargaɗin aukuwar tsunami a fadin yankin, kamar yadda kafofin watsa labarai suka ba da rahotonsa, inda suka ambato hukumar kula da halittu da ruwa da ƙasa na Amurka (USGS).
Mai magana da yawun ofishin hukumar ba da agajin gaggawar Diego Mariano ya ce an yi mace-mace ciki har da mutum uku daga lardin Davao Occidental, uku daga birnin General Santos City kuma biyu daga lardin South Cotabato.
Adadin bai haɗa da mutum biyun da Manjon ‘Yansanda Roland Catoburan ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP benen da ya faɗo ya murƙushe su a Alabel, wani gari kusa da General Santos, ba.
Za a iya samun igiyoyin ruwan Tsunami sun kai fiye da mita 3 (ƙafa 10 ) sama da matakin ruwa a wasu yanki na gaɓar tekun Philippine biyo bayan gagarumar girgizar ƙasar da ta auku a cikin ruwa kusa da gundumar Sarangani na tsibirin Mindanao, in ji cibiyar gargaɗin Tsunami ta Amurka a kan yankin Pacific.
Cibiyar bincike kan ilimin yanayin duniya na Jamus (GFZ) ta ba da rahoton cewa girgizar ƙasar da ta afka wa Mindanao a wani wuri mai nisan kilomita 10 (mil 6.2) kuma ya sa tsananin girgizar zuwa maki 8.2.
Tsakiyar inda girgizar ƙasar ta afka wa ya kai kilomita 24.7 (mil 15.3) yamma maso kudancin Burias, a Philippines, kuma yana da zurfin kilomita 35 (mil 22 ). An yi girgizar ƙasan ne da misalin ƙarfe 7:37 na safiya.
“Ku tafi wuri mai tudu yanzu”
Wani motsin ƙasa mai ƙarfin maki 6.1 bayan girgizar ƙasar ya afka wa yankin kimanin sa’o’i biyu bayan girgizar ƙasa ta farko, in ji hukumar USGS.
Cibiyar ba da gargaɗin Tsunami ta yankin Pacific ta bayyana a wata sanarwa cewa za a iya samun igiyoyin tsunami "cikin sa’o’i uku masu zuwa" a bakin tekun ƙasashen Philippines da Indonesia da Palau da Taiwan da Papua New Guinea.
Hukumar sufurin jiragen sama ta Philippines ta dakatar da ayyuka na wucen gadi a filin jiragen sama na General Santos biyo bayan girgizar ƙasar da kuma gargaɗin tsunami da Phivolcs ta bayar.
Hukumomi a Philippines da Indonesia sun yi kira ga mazauna yankunan bakin tekun da lamarin ya shafa su koma wurare masu tudu nan-take.
"A halin yanzu , akwai rahoton mutuwar mutum ɗaya da kuma mutum huɗu da suka ji rauni. Wannan rahoto na farko ne kawai," kamar yadda Masta Sajent Robert Dagon na rundunar ‘yansandan birnin General Santos City ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.
"Wasu gine-gine sun rufta," a cewarsa.
"Gine-gine da yawa ne lamarin ya shafa, amma ba zan iya ƙirga su ba a halin yanzu saboda mun shagaltu da ceton da ake yi."
Shugaban Philippine Ferdinand Marcos ya dakatar da azuzuwan makarantu a wuraren da lamarin ya shafa a Mindanao yayin da yake kira ga mazauna bakin teku su ƙaurace nan take.
"Ku tafi wurare masu tudu a yanzu. Kada ku jira," a cewarsa. "Rayukansu sun fi duk abin da kuka bari a baya muhimmanci."
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Indonesia, ta ba da umarni ga jami’ai a babban birnin lardin North Sulawesi, da Manado da arewacin Gorontalo da kuma tsibiran Sangihe "su bai wa mazauna garuruwansu su ƙaurace yadda ya kamata zuwa wurare masu tudu".
Philippines, ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi bala’i, yana yawan samun girgizar ƙasa da kuma aman wuta domin kasancewarta a kan “zoben wutar” yankin Pacific, wani bakan na yiwuwar girgizar ƙasa a kewayar tekun.
Hukumomin Japan sun ba da wata shawara game da tsunami ga wasu yankuna na bakin tekun Pacific, inda suke hasashen yiwuwar samun igiyoyin ruwa da suka kai mita ɗaya (ƙafa 3.28 ) da za su afka wa yankuna daban-daban daga ƙarfe 11:30 na safiya na yankin (ƙarfe 02:30 kenan agogon GMT).
Igiyar tsunami mai tsawon mita ɗaya zai iya kai ga tsibirin Yaeyama a Okinawa kamar yadda kamfanin dillancin labaran Kyodo ya ruwaito, yana mai ambato hukumar hasashen yanayi ta Japan.














