Wani hatsarin motar bas a yankin gabashin Sinai na Masar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 16 tare da raunata wasu 28 a ranar Laraba, in ji ma'aikatar lafiya ta kasar.
Motocin daukar marasa lafiya guda 20 sun yi gaggawar zuwa wurin da hatsarin ya faru, tsakanin garuruwan yawon bude ido masu shahara na Dahab da Nuweiba a gabar tekun Kudancin Sinai, in ji ma'aikatar.
Wadanda abin ya shafa sun hada da mutane 10 daga Jordan, a cewar gidan talabijin na masarautar.
"Mutane goma 'yan kasar Jordan sun mutu bayan da wata motar fasinja ta kife a kan hanyar Dahab-Nuweiba a yankin kudancin Sinai na Masar," in ji Tashar Al-Mamlaka ta gwamnatin Jordan, tana mai cewa motar tana dauke da mutane 43 jimilla kuma 22 daga cikin su 'yan kasar Jordan ne.
Hukumomi sun ce wadanda suka jikkata suna karbar kulawar lafiya, amma ba su bayyana musabbabin hatsarin ba.
Yankin wuri ne da yawon bude ido ya shahara, wanda aka san shi da bambancin halittu na ruwa, kyawun halitta da hanyoyin hawa duwatsu.
A watan da ya gabata, akalla mutane 18, da yawa daga cikinsu matasa ne, sun mutu a arewacin Masar lokacin da manyan motoci biyu masu daukar kaya dauke da ma'aikatan noma suka yi hatsari.
A bara, kusan mutane 6,000 ne suka mutu a hadurra a kan tituna a fadin kasar, a cewar hukumar kididdiga ta kasar Masar.

















