| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Hatsarin mota ya kashe mutum 22, ciki har da sojoji 17 a Nijar
Ministan Sufurin ƙasar Kanal-Manjo Abdourahamane Amadou ya ce zai gayyaci kamfanonin STM da SONITRAV, waɗanda a tsakanin motocinsu ne hatsarin ya auku, su bayyana a ofishinsa ranar Litinin
Hatsarin mota ya kashe mutum 22, ciki har da sojoji 17 a Nijar
Sojojin Nijar 17 na cikin mutum 22 da suka rasu nan-take a hatsarin motar da ta faru a ƙasar

Mutum 22 sun mutu nan-take, ciki har da sojoji 17 yayin da mutum 37 suka ji rauni a wani hatsarin motar da ya faru kan hanyar Maradi zuwa Madaoua da ke jihar Tahou a ƙasar Nijar.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar (ANP) ya ruwaito cewa lamarin ya auku ne ranar Jumma’a da misalin ƙarfe takwas na safiya.

Kamfanin dillancin labaran ANP ɗin ya ambato wata sanarwa daga ma’aikatar Sufirin ƙasa da saman ƙasar tana cewa lamarin ya auku ne yayin da wata motar bas ta kamfanin STM da ke tahowa daga Madaoua ta yi taho-mu-gama da wata bas ta kamfanin SONITRAV da ke tahowa daga Zinder ɗauke da jami’an sojoji da suka kammala horarwarsu.

Ministan Sufurin ƙasar Kanal-Manjo Abdourahamane Amadou ya ce zai gayyaci kamfanonin STM da SONITRAV, waɗanda a tsakanin motocinsu ne hatsarin ya auku, su bayyana a ofishinsa ranar Litinin domin bin ba’asin abin da ya faru, in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar, ANP.

“Nauyin tsaron da kuma amincin fasinjoji ya rataya ne kan kamfanonin sufuri. Saboda haka ya zama wajibi waɗannan kamfanonin su bi ƙa’idojin aminci na yanzu su tabbatar da gyara motocinsu a-kai-a-kai da kuma biyayya ga dokokin da ke da alaƙa da tuƙi da kuma hutun direbobi," in ji sanarwar ma’aikatar da ANP ta ambato.