Taron ƙawancen NATO a Ankara na wannan makon zai nuna wa Shugaban Amurka Donald Trump cewa ƙawaye na Turai suna yunƙurwowa domin ba da gudunmawa don ƙarin ƙarfi ga ƙawancen, kamar yadda mataimakin ministan tsaron Jamus ya bayyana.
“Trump zai iya tabbatar da cewa daukar nauyi ba take ba ne kawai, ɗaukar mataki ne, kuma mun ga wannan ba a Jamus kaɗai ba, amma a cikin sauran ƙasashe mambobi na Turai ,” kamar yadda Nils Schmid ya bayyana a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da kamfanin dillancin labaran Anadolu.
“Muna tsammanin taron Ankara zai tura wata bayyananniyar alama ta haɗin kai mai ƙarfafa dangantaka da ta eta tekun Atalantika da kuma bayyana cewa daga dukkan ɓangarorin Atalantika, ƙawancen NATO shi ne babban madogarar tsaro ta haɗaka.”
Taron ranar 7 zuwa 8 na watan Yuli a babban birnin Turkiyya zai haɗa shugabanni daga mambobin NATO, tare da manyan kwamandojin soji da ministocin tsaro da na harkokin waje. Shawarar da Trump ya yanke ta halartar taron, bayan watanni na tsamin dangantaka da ƙawayen ƙasarsa na Turai, ta ƙara wa taron muhimmanci.
Da yake mayar da martani ga kakkausar sukar Trump cewa ƙawaye na Turai ba sa ba da isasshen gudumowa ta kuɗin kayan sojin da NATO ke kashewa, Schmid ya ce mambobi sun fara ƙara kuɗin da suke warewa ga harkar tsaro a kasafin kuɗaɗensu kuma suna kan hanyarsu ta cim ma abin da ta tsara wa kanta a taron na NATO na shekarar 2025 a birnin Hague.
Shuwagabanni sun yarda su ƙara mafi ƙaranci na kuɗin da ya kamata a ware ga tsaro zalla zuwa aƙalla kashi 3.5 cikin 100 na kimar tattalin arziki a ma’aunin GDP, daga kashi 2 cikin 100.
“Za ni so na bayyana cewa dukkan ƙawaye na Turai a halin yanzu sun wuce mataki na ware kashi 2 cikin 100 [kan tsaro], wanda aka tsara a lokacin da ya gabata a taron NATO, kuma a halin yanzu ƙarin ƙawaye na Turai suna kan hanyarsu ta kawo kuɗaɗen da suke kashewa kan soji zuwa kashi 3.5 cikin 100 na GDP,” a cewar Schmid .
“Da gaske , akwai bambance-bambance a faɗin ƙasashe mambobi na Turai , Amma za ni iya gaya maka cewa Jamus , a matsayinta na ƙasa ta biyu da ta fi ƙarfin tattalin arziki a cikin ƙawancen NATO bayan Amurka US, a halin yanzu ta shirya domin ta cim ma wannan manufa nan da shekarar 2029, gabbanin ranar da aka saka [domin cim ma manufar], wadda ita ce shekarar 2035,” a cewarsa.
A taron Ankara , ana tsammanin ƙawayen su sake nazari kan ci-gaban da aka samu kan waɗannan manufofi na kashe kuɗi yayin da ake neman ƙarin haske game da muhimman batutuwa , ciki har da makomar tabbacin tsaron da Amurka ke yi wa Turai , yiwuwar sauyi a kan adadin dakarun Amurka a nahiyar , da kan ko Washington za ta ci gaba da samar da ikon soji domin tallafa wa tsaron Turai.
Tattaunawar na zuwa ne ‘yan makonni bayan sakataren tsaro na Amurka Pete Hegseth ya yi shelar cewa wani bincike na “NATO 3.0 review” da ma’aikatar Pentagon ta yi game da sojin Amurka a Turai, wanda ya ce zai gaggauta wani sauyi “mai sauri da ba za a iya mayar da shi baya ba” zuwa ga samun ƙarin dogaro da kai na Turai da kuma bai wa dakarun Amurka damar magance ababen da aka fi buƙatar magance su a duniya.
Turai na nemna jadawali na janye dakarun Amurka
Schmid ya ce shekar da gwamntin Trump ta yi cewa tana shirin rage adadin dakarunta a Turai bai zo da mamaki ba.
Ya bayyana cewa gwamnatocin Amurka na baya su ma sun nuna irin wannan sauyin yayin da hankalin Washington ya tashi daga Turai zuwa yankin Indiya da Pacific.
Ƙawayen Turai suna shirin magance duk wani giɓi da zai iya biyo baya cikin jami’ai da kayayyakin aiki, a cewarsa , amma ya jaddada cewa dole a bi duk wani raguwan ababe a hankali .
“Game da ƙwarewa, muna da ƙwarin gwiwa cewa ‘yanTurai za su iya aiki tare domin cike giɓi da zai iya fitowa cikin shekaru da ke zuwa ,” in ji shi .
“Abu mai muhimmanci shi ne muna yin wannan ne cikin wani yanayi na haɗin gwiwa tsakanin ƙawaye , abin da ke nufin ya kamata a ce mu mambobin ƙawancen NATO na da tsarin aiki a Turai , [kan] idan da kuma lokacin da za janye muhimman kayayyakin Amurka, kayayyakin soji, .”
'NATO za ta ƙara dacewa da Turai '
Schmid ya ce Jamus tana aiki da ƙawayenta na Turai a ƙawancen NATO da abokanai na Tarayyar Turai domin ɗaukar sabon mataki —lamarin da zai haɓaka ikon sojin Turai , da zurfafa hadin kai na masana’antar tsaro da kuma gaggauta ƙera ingantattun makamai .
“Muna buƙatar NATO ta ƙara dacewa da Turai soboda ta iya ci gaba da kasancewa dangataka mai ƙarfi mai ƙetare tekun Atalantika,” in ji shi , yana mai ƙarawa da cewa sabbin tsare-tsare na tsaron Tarayyar Turai ya kamata su taimaka wa, maimakon maimaita kayayyakin ayyukan NATO.
Ya jaddad cewa irin waɗannan matakan ya kamata su kansance masu haɗa kowa, da za su ba da damar haɗin kai da ƙasashen ƙawancen NATO da ba sa cikin Ƙungiyar Tarayyar Turai.
“Gare mu, yana da muhimmanci mu kasance muna da wuraren haɗa kai da ƙawayen NATO [ƙawaye ] waɗanda ba mambobin Ƙungiyar Tarayyar Turai ba ne . Kuma ina da ƙwarin gwiwar cewa ƙawaye [mambobi] ƙasashe irin su Birtaniya da Norway, amma da kuma Turkiyya za su iya kasancewa masu taimakawa sosai game da wannan ,” in ji shi.
“Tun da a halin yanzu muna cikin ƙarancin lokaci, abin da ke nufin cewa NATO na shiryawa domin kwanan watan shekarar 2029 … Wannan shi ya sa a gare mu , haɗa kai da mambobin NATO da ba sa cikin Ƙungiyar Tarayyar Turai na cikin lamarin ,” in ji shi .
‘Yansiyasan yawanci suna ishara ga shekarar 2029 a matsayin muhimmin kwanan wata saboda nazarin sojin NATO na nuna cewa Rasha za ta iya, nan da ƙarshen shekarar 2030, yin ƙarin barazana kai tsaye, da yiwuwar iya kai hari kan wata mambar ƙawancen NATO a gabashin Turai.











