| hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Geoffrey Nnaji: Ministan Kimiyya da Fasaha na Nijeriya ya yi murabus kan takardar digiri ta bogi
Hukumomi a Jami’ar UNN da ke Nsukka sun ce duk da cewa Geoffrey Nnaji ya fara karatu a jami’ar a shekarar 1981 amma bai kammala karatun digirinsa ba.
Geoffrey Nnaji: Ministan Kimiyya da Fasaha na Nijeriya ya yi murabus kan takardar digiri ta bogi
Geoffrey Uche Nnaji ya ajiye aiki ne bayan an zarge shi da amfani da takaradar digiri na boge
8 Oktoba 2025

Ministan Kimiyya da Fasaha na Nijeriya, Geoffrey Uche Nnaji, ya sauka daga muƙaminsa bayan rahotanni sun ce ya yi amfani da ta takardar shaidar digiri ta boge.

Wata sanarwar da mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata, ta ce shugaban ya amshi takardar barin aikin ministan.

“Shugaba ya naɗa Nnaji a muƙamin minista ne a watan Agustan shekarar 2023. Ya ajiye aiki a yau a wata wasiƙa inda ya gode wa shugaban kan damar da ya ba shi ta yi wa Nijeriya hidima,” in ji sanawar.

“Nnaji ya ce abokan adawarsa na siyasa ne ke masa bi-ta-da ƙulli. Shugaba Tinubu ya gode masa kan hidimarsa kuma ya yi masa fatan aheri,” in ji Onanuga.

Matsalar da Nnaji ya fuskanta ta kunno kai ne bayan rahotanni sun ce ministan bai kammala karatun digiri ba a Jami’ar UNN ta Nsukka, wadda ya gabatar da takardar shaidar digirinta a lokacin tantance shi domin ba shi muƙamin minista.

Hukumomi a Jami’ar UNN da ke Nsukka sun ce duk da cewa Geoffrey Nnaji ya fara karatu a jami’ar a shekarar 1981 amma bai kammala karatun digirinsa ba.

Kazalika hukumar da ke kula da yi wa ƙasa hidima ta Nijeriya (NYSC) ta ce ministan bai yi wa ƙasar hidima ba, lamarin da ya sa aka ce takardar shaidar yi wa ƙasa hidimar da ya yi amfani da ita ma ta bogi ce.  

Rumbun Labarai
Nijeriya ta dakatar da aiwatar da harajin kashi 15% kan shigar da fetur da dizal cikin ƙasar
'Musulmai ne Boko Haram ta fara yi wa ɓarna': AU ta yi watsi da Trump kan kisan kiyashi a Nijeriya
Za mu bai wa kowane jami'in soja da ke bakin aikinsa kariya  - Ministan Tsaron Nijeriya
An kama hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1,000 a Nijeriya
‘Yan wasan Super Eagles sun ƙaurace wa atisaye kan rashin biyansu alawus
Jiragen yaƙin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP da ɓarayin daji a Borno da wasu jihohin Arewa
Babu abin da za mu rasa idan Nijeriya ta daina hulɗa da Amurka – Sheikh Gumi
Damuwa kan kutsawar 'yan bindiga Jihar Kano
Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta kuɓutar da mutum 86 da Boko Haram ta yi garkuwa da su
INEC ta ayyana Charles Soludo na APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Anambra
Gwamnatin Nijeriya ta amince a ci bashin dala 396 domin inganta kiwon lafiya da ayyukan jinƙai
An gabatar da kudiri a Majalisar Dokokin Amurka don saka wa Ƙungiyoyin Miyetti Allah takunkumi
‘Kisan kiyashi ga Kiristoci: Me ya sa kurarin Trump a Nijeriya yake kan kuskure da rashin dacewa?
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince a ɗaure malaman makaranta shekara 14 kan cin zarafin ɗalibai
An kashe 'yan ta'adda fiye da 592 a Borno tun daga Maris din 2025 - Ministan Yada Labaran Nijeriya
ECOWAS ta yi tir da ikirarin ‘ƙarya mai hatsari’ na Amurka cewa Nijeriya ta bari ana kashe Kiristoci
Hukumar DSS a Nijeriya ta kori ma'aikatanta fiye da 100
Amurka na da ajanda a Nijeriya tana fakewa da kisan Kiristoci - Sheik Bala Lau
China na adawa da Trump kan amfani da 'addini da ‘yancin ɗan'adam' domin tsoma baki a Nijeriya
Naira da hannayen-jari Nijeriya sun faɗi sakamakon barazanar da Trump ya yi ta kai hari ƙasar