Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da kashi na biyu na shirin takardun lamuni na naira biliyan 729 (Series 2 Power Sector Bond), domin biyan basussukan da ake bin fannin wutar lantarki tare da inganta samar da lantarki a faɗin ƙasar.
Ministan Kuɗi kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ne ya sanar da hakan yayin wani taron masu zuba jari da aka gudanar a Abuja.
Ya ce sabon bashin ya biyo bayan bashin farko na naira biliyan 520, wanda aka saye gaba ɗaya kuma an riga an fara biyan kuɗaɗen da suka shafe shi.
A cewarsa, shirin lamunin wani ɓangare ne na Shirin Shugaban Ƙasa na Rage Basussukan Fannin Wutar Lantarki, kuma za a yi amfani da kuɗaɗen wajen biyan basussukan da aka tantance na kamfanonin samar da wutar lantarki da masu samar da iskar gas.
Oyedele ya bayyana cewa matakin zai taimaka wajen inganta kuɗaɗen gudanar da harkokin fannin, ƙara yawan wutar da tashoshin lantarki ke samarwa, da kuma dawo da amincewar masu zuba jari.
Ministan ya kuma danganta wannan gyara da bunƙasar tattalin arzikin ƙasar, yana mai cewa tattalin arzikin Nijeriya ya samu ci gaban kashi 3.9 cikin 100 a rubu'in farko na shekarar 2026.
Ya yi kira ga masu zuba jari da su ci gaba da haɗa gwiwa da gwamnati yayin da take ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziki da kuma jawo dogon zuba jari cikin ƙasar.
















