Abin da ya sa Afirka ke son a amince da cinikin bayi da mulkin mallaka a matsayin kisan kiyashi

Wani mataki mai muhimmanci da aka amince da shi a wajen Taron AU na 39 ya fayyace zaluncin da aka yi ta hanyar cinikin bayi da mulkin mallaka a mahangar dokokin kasa da kasa, amma kwararru sun yi gargadin cewa batun na iya zama sanarwar kawai.

By
Bayi 'yan Afirka kenan yayin da ake saka su a jirgin ruwa don kai su Amurka. / Photo: Getty Images / Getty Images

Akalla 'yan Afirka miliyan 12.5 ‘yan kasuwar Turai suka yi garkuwa da su tare da sayar da su a matsayin bayi a tsakanin ƙarni na 15 da 19.

Ƙasashen Turai da suka zana nahiyar daga baya sun lalata shugabancin 'yan asalin ƙasashen, sun kwaci dukiya a fannin masana'antu kuma suka sake gina iyakoki ba tare da la'akari da mutanen da ke zaune a yankunan ba.

A taron kolinsu na 39 da aka yi a Addis Ababa daga ranar 11 zuwa 15 ga Fabrairu, Tarayyar Afirka ta ba wa wannan mummunar ta’asa da aka yi a wadancan karnikan da: kisan kare dangi.

Wannan mataki ya wuce abin da aka saba gani a cikin irin waɗannan kudurori. "Yana wakiltar amincewar hukumomi kan cewa waɗannan tsarin ba wai kawai ayyukan cin zarafi ba ne, wasu ayyuka ne da aka tsara na kawar da ɗan adam, ƙwace dukiya da kuma lalata al'ummomin Afirka," in ji marubuci kuma masanin kimiyya Therence Atabong Njuafac, wanda ya ƙware a hulɗar ƙasa da ƙasa da kimiyyar siyasa, yayin tattaunawa da TRT Afrika.

Atabong ya ɗauki ƙudurin a matsayin gyara mai zurfi, yana ƙalubalantar labaran da suka tsara tashin hankalin mulkin mallaka a matsayin manufa mai wayewa da kuma mai da hankali kan ƙwarewar tarihi ta Afirka a cikin tattaunawar adalci ta duniya.

Macharia Munene, farfesa a fannin kimiyyar siyasa a Jami'ar Nairobi, ya yi imanin cewa kudurin ya sanya matsayin Afirka na haɗin gwiwa kan cinikin bayi na tsawon ƙarni da mulkin mallaka a yankin Atlantika ya zama a fayyace karara.

"A matsayin wakiliyra nahiyar, AU na iya buƙatar diyya daga dillalan bayi da masu mulkin mallaka," ya fada wa TRT Afrika.

Wajabcin daukar matakin

Shugaba John Dramani Mahama na Ghana, wanda ya gabatar da kudurin, ya kira amincewa da shi wani muhimmin lokaci da mutanen Afirka suka daɗe suna jira.

"Ba za a iya binne gaskiya ba. Dalilai na shari'a na da karfi; ba za a iya musanta abin da ya faru ba," in ji shi a wajen taron kolin.

Mahama ya fito da gaskiyar tarihi da ke fuskantar juna a matsayin aikin jarumtaka na ɗabi'a maimakon rarrabuwa, yana mai lura da cewa tasirin bauta ya ci gaba a yau a cikin rashin daidaiton tsari, wariyar launin fata da rashin daidaiton tattalin arziki.

"Mataki na farko zuwa ga warkarwa shi ne darar gaskiya. Dole ne a faɗi gaskiya game da labarin cinikin bayi na trkin transatlantic," in ji shi, yana mai bayyana kudurin a matsayin mataki na farko.

Ta hanyar bayyana bautar da mutane da mulkin mallaka a matsayin laifukan kisan kare dangi, AU ta sake tsara su a cikin ƙa'idojin doka da ɗabi'a na duniya na zamani.

Atabong ya bayyana cewa fahimtar munanan abubuwa na tarihi a tare yana tabbatar da abubuwan da suka faru na al'ummomin Afirka da na ƙasashen waje.

"Yana tabbatar da cewa rashin ci gaban tattalin arziki, rashin daidaiton siyasa, da rashin daidaiton launin fata da ake gani a yau ba abubuwa ne na kwatsam ba. An samar da su a tarihi," Ya shaida wa TRT Afrika.

Batun biyan diyya

Idan wata ƙungiyar nahiya da ke da ƙasashe 55 mambobi ta yi magana da murya ɗaya, hakan yana canza yanayin tattaunawar duniya game da alhakin tarihi da rashin daidaito a tsarin mulki.

Sarki Charles na Birtaniya ya yi magana game da nadamarsa game da bauta da kuma goyon bayan bincike kan alaƙar tarihi da masarautar Birtaniya ke da ita da cinikin bayin. Birtaniya ce ke da alhakin jigilar mutane kimanin miliyan 3.2 a matsayin bayi, wanda hakan ya sanya ta zama ƙasa ta biyu mafi aika-aika a Turai bayan Portugal, wadda ta bautar da kusan miliyan shida.

Sakatariyar ƙungiyar Kasashe Rainon Ingila ta Commonwealth Shirley Botchwey, tsohuwar ministar harkokin wajen Ghana wacce ta goyi bayan diyya daga Birtaniya a bainar jama'a, tana goyon bayan ƙasashen mambobi kan batun neman diyya.

"A fahimtata ita ce akwai wasu shirye-shirye dangane da samun ƙungiyoyi a teburin da za su yanke shawara kan hanyar da za a bi, gami da nau'ikan diyya daban-daban da kuma yadda za a ci gaba da waɗannan ayyukan" ta shaida wa Reuters.

Domin adalcin biyan diyya ya zama gaskiya, Munene ya bayar da shawarar cewa ƙasashen Afirka su kafa ƙungiyar masu fafutuka don shirya gangamin.

Atabong ya gabatar da shawarar cewa ƙasashen Afirka su kafa wani kwamiti mai girma na masana shari'a da masana tarihi "don samar da cikakken tsarin shari'a da shaidu da ke nuna girman kisan kare dangi na bauta da mulkin mallaka".

Nahiyar kuma tana buƙatar samar da haɗin gwiwa na diflomasiyya tare da ƙasashen Caribbean, ƙasashen Latin Amurka da al'ummomin ƙasashen waje waɗanda tarihinsu ke da alaƙa kai tsaye da tsarin cinikin bayi na transatlantic.

Masu sharhi sun yi hasashen cewa wani dandamali mai tsari na Duniya ta Kudu zai yi tasiri sosai a tattaunawar ƙasa da ƙasa.

Sabon kudurin AU ya ambaci cewa za a yi bikin ranar 30 ga Nuwamba a matsayin Ranar Godiya, don girmama waɗanda aka zalunta sakamakon rashin adalci na tarihi.

A zahiri, tasirin zai dogara ne akan bin diddigin lamarin. Atabong ya yi gargaɗin cewa kudirin yana da hatsarin kasancewa alama ba tare da wayar da kan jama'a da dabarun diflomasiyya masu tsari don aiwatarwa ba.