| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya za ta jagoranci tallafin jinƙai yayin da tsarin tallafin MDD yake sauyawa, a cewar minista
Nijeriya na shirin ɗaukar babban nauyi wajen tsara tallafin jinƙai a cikin ƙasar, yayin da take kauce wa tsarin da mafi yawanci ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa ne suke jagorantarsa.
Nijeriya za ta jagoranci tallafin jinƙai yayin da tsarin tallafin MDD yake sauyawa, a cewar minista
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan 'yan Najeriya miliyan 35 na fuskantar barazanar yunwa a shekarar 2026.

Hukumomin Nijeriya sun ce ƙasar na shirin ɗaukar babbar nauyi wajen bayar da agajin jinƙai a cikin ƙasar, yayin da take sauyawa daga tsarin da mafi yawanci masu ba da tallafi na ƙasashen waje da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta.

An bayyana wannan mataki a wani taron haɗin gwiwa a kan sauyin a babban birnin ƙaar Abuja a ranar Talata, inda gwamnatin Nijeriya da Majalisar Dinkin Duniya suka fara tattaunawa kan miƙa mafi yawan alhakin tsarawa, daidaitawa, da kuma ɗaukar nauyin kuɗaɗen ayyuka ga cibiyoyin ƙasa.

Ministan jinƙai na Nijeriya, Bernard Doro, ya ce wannan ba wata janye tallafin ƙasashen waje ba ce, amma sauyi ne zuwa tsarin da gwamnati ke jagoranta wajen daidaitawa, wanda zai ci gaba da samun tallafin ƙwararru daga Majalisar Dinkin Duniya da sauran abokan hulɗa.

Jami’in MDD Mai Tsara Ayyukan Jinkai, Mohamed Fall, ya ce shawarar ba ta rage tallafi ba ce, sai dai sauyi zuwa sabon tsari wanda zai amfana da ƙarin kuɗaɗen gwamnati da na sashen masu zaman kansu don ƙarfafa tallafin jinƙai.

Shirye-shirye, martani, da farfaɗowa

Kuɗaɗen da masu ba da tallafi ke bayarwa na fuskantar ƙarin matsin lamba a duniya, yayin da Nijeriya ke son ƙarfafa ikonta na mayar da martani ga rikice-rikice, da ƙaura, da rashin abinci, da ambaliya, da matsalar yanayi, da matsalolin lafiyar jama'a.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutane miliyan 35 a Najeriya na fuskantar barazanar yunwa a wannan shekara bayan koma bayan kasafin kuɗaɗen agaji na duniya.

Doro ya ce ma'aikatarsa za ta yi aiki tare da hukumomin tarayya da na jihohi, da ƙungiyoyin agaji da al'ummomin da abin ya shafa don tsara shirye-shiryen jinƙai, da martani, da ayyukan farfado da jama’a a faɗin ƙasar.

Ya ce Najeriya na da niyyar jagorantar ƙirƙirar shirin jinƙai na 2027, tare da tallafin ƙwararru daga hukumar OCHA da tsarin Majalisar Dinkin Duniya gabaɗaya.

Rumbun Labarai
‘Yansandan Nijeriya 10 sun rasa rayukansu a musayar wuta da mahara a arewacin ƙasar, in ji hukumomi
'Yan Nijeriya sun kashe Naira tiriliyan 6.6 kan sayen datar waya a cikin shekara ɗaya
Mutane 237 ne suka mutu sakamakon zazzaɓin Lassa a watanni bakwai na 2026 a Nijeriya - NCDC
Sojojin Nijeriya sun kashe Abu Khalid Al Muhajir da wasu  kwamandojin ISWAP tara a Borno
Masarautar Kano ta musanta bidiyon da ake yadawa kan Sarki Sanusi II ya samu 'carry-over' a jami'a
Super Falcons da Indomitable Lionesses na gogayyar shiga Gasar Kofin Duniya
Gwamnatin Nijeriya za ta fara sarrafa kayayyakin tsara iyali a cikin ƙasar
Hukumar EFCC ta rufe asusun gwamnatin Jihar Osun kwanaki kaɗan kafin zaɓen gwamna
Rundunar sojin Nijeriya ta sanya tukuicin N60m kan kwamandan ISWAP da mataimakinsa
An yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja
An saki gomman mutanen da aka yi garkuwa da su a Jihar Kwara bayan wata shida a hannun ‘yanta'adda
WAEC ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 167,486
Dakarun Nijeriya sun kama mutanen da ake zargi da kai wa  'yan Boko Haram ƙwayoyi a Borno da Yobe
Gwamnati ta ba jami’o’i da kwalejojin Nijeriya umarnin korar ɗalibai da ke da alaka da satar mutane
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum 48 a samamen da suka kai maɓoyar masu laifi a Zamfara
An saki alƙalin da aka yi garkuwa da shi a jihar Kebbin Nijeriya
Dakarun Nijeriya sun daƙile harin daren 'yanta'adda kan sansanin soji
'Yanbindiga sun kashe mutum 12, sun yi garkuwa da mata da yara a wani ƙauye Sokoto a Nijeriya
Nijeriya ta tura sojoji 86 domin aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau
Sojojin Nijeriya sun daƙile yunƙurin 'yanta'adda na garkuwa  da mutane 31 a Borno