Mahaifin kyaftin din Super Eagles Wilfred Ndidi ya mutu sakamakon hatsarin mota

Sunday Ndidi ya rasu da safiyar Talata bayan hatsarin mota a garin Umunede a Jihar Delta, in ji Tarayyar Kwallon Kafa ta Nijeriya.

By
Sunday Ndidi ya rasu da safiyar Talata bayan hatsarin mota a garin Umunede na Jihar Delta / Reuters

Kyaftin ɗin tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Wilfred Ndidi, ya rasa mahaifinsa a hatsarin mota da ya faru ‘yan makonni bayan da Ndidi ya jagoranci tawagar wajen samun matsayi na uku a Gasar Kofin Afirka ta AFCON 2025.

Ademola Olajire, daraktan hulɗa da jama'a na Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya, NFF, ya shaida wa The Associated Press cewa, Sunday Ndidi ya mutu a safiyar Talata bayan wani haɗari a garin Umunede na Jihar Delta, a kudancin Nijeriya.

Wilfred Ndidi mai shekaru 29, ya rubuta a labarin Instagram game da tattaunawarsa ta ƙarshe da mahaifinsa safiyar Talata: 'a cikin muryarka akwai murna amma a can ƙasa ashe bankwana kake min... To yaya abubuwan da muka tattauna, ba za mu sake magana ba? Sai dai tunawa kawai?'

Ndidi ya ambaci yadda ya yi murnar tunawa da mahaifinsa bayan ya zura ƙwallo a Gasar Kofin Afirka, a wasan da suka doke Tunisia 3-2 a zagayen rukuni.

Ndidi ya rubuta cewa, “Ko lokacin da na zura ƙwallota ta farko a tawagar ƙasa, na yi maka rawar Papilo, amma kai kawai za ka so hakan...”.

Hukumar NFF ta yi ta'aziyya a dandalin sada zumunta na X, a wani rubutu da ta ce, 'Muna tare da kai da iyalanka da addu'o'inmu a wannan mawuyacin lokaci, Wilfred.'

Kulob ɗin da Ndidi ke buga wasa a Turkiyya, Beşiktaş, shi ma ya yi amfani da shafin X don miƙa ta'aziyya.

Ƙungiyar da ke birnin Istanbul ta rubuta cewa, “Muna matuƙar baƙin ciki da jin labarin rasuwar mahaifin ɗanwasanmu Wilfred Ndidi, Sunday Ndidi, a wani mummunan haɗarin mota”.

A ƙarshen watan Disamba ma, tsohon zakaran boksin na duniya, Anthony Joshua, ya samu rauni a wani hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu daga cikin abokansa a kusa da Legas.