Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda tare da ƙwace makamai a Jihar Filato

Duk da kafiyarsu daga farko, ƙarfin makaman sojojin ya rinjayi ‘yanta’addan daga baya inda aka kashe 10 daga cikinsu yayin da wasu suka tsere cikin dazukan da ke kusa, in ji sanarwar.

By
Sojin Nijeriya na yaƙar ta'addanci a sassan Nijeriya ciki har da cihar filato dake tsakiyar ƙasar / AFP

Dakaru na musamman na rundunar Operation Enduring Peace da ke aikin wanzar da tsaro a jihar Filato da ke tsakiyar ƙasar da ‘yan sa-kai sun yi nasarar kashe ‘yanta’adda goma a wani aikin kakkaɓe masu aikata laifuka da suka yi a ƙauyukan Daba da Seri da ke ƙananan hukumomin Wase da Kanam.

​Wata sanarwa da jami’in watsa labarai na rundunar, Kyafin Chinonso Polycarp Oteh, ya fitar ranar Jumma’a ta ce dakarun rundunar sun ƙaddamar da aikin ne da safiyar ranar Alhamis 9 ga watan Afrilun shekarar 2026 inda suka toshe wasu hanyoyi masu muhimmanci tsakanin Dutesen Zaki da Dajin Odare.

“Yayin aikin, an ga gungun ‘yanta’adda bisa babura inda suke tafiya a wata sananniyar hanyar daji, kuma nan-take dakarun suka yi arangama da masu aikata laifukan inda suka rinjaye su da ƙarfin makamansu,” in ji sanarwar.


Duk da kafiyarsu daga farko, ƙarfin makaman sojojin Nijeriya ya rinjayi na ‘yanta’addan daga baya inda aka kashe 10 daga cikinsu yayin da wasu suka tsere cikin dazukan da ke kusa, in ji sanarwar.

A wani batu makamancin hakan, bayan wani rahoto na wani hari kan matafiya a kan hanya a Razat da Kafi Abu, dakarun Nijeriya sun ƙaddamar da hari na gaggawa kan masu aikata laifuka.

Fara arangamar ke da wuya sai masu aika-aikar suka janye zuwa dazukan da ke kusa inda jami’an tsaro suka bi su nan-take domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

​Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun sun ƙaddamar da bincike a ƙauyukan Suma Suga da Takwok , da kuma wuri mai tsaunuka da ke kusa da su.

Wannan ya sa dakarun sun gano kayayyakin da masu aikata laifukan suka bari a baya ciki har da bindigogi ƙirar AK-47 guda uku da harsasai da sauransu.