Makomarmu ba ta sayarwa ba ce: Abin da ya sa dole matasan Afirka su nemi ba’asin haraji da cin bashi
An koya mana cewa kakaba haraji na gina hanyoyi da makarantu. Amma me ke faruwa yayin da bashin ya lalace zuwa marar ma’ana da kashe kudaden da ba a bin ba’asi?
A shekarar da ta gabata, duniya ta shaida wani sabon juyin juya hali na Afirka da ke faruwa ba a fagen daga kawai ba, har ma a shafukan sada zumunta da titunan manyan biranenmu.
A Nairobi, matasan Kenya sun mamaye Majalisar Dokoki don nuna kin amincewa da Dokar Kudi ta 2024. A Abuja, matasa sun yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa. A Kampala, masu fafutuka sun yi zanga-zanga kan cin hanci da rashawa. A Mozambique da Madagascar, matasa sun fita titunan kasashen.
Ga masu lura da al'amura, matasan sun bayyana cikin matsananciyar damuwa. Amma tsintsiyar manufa guda daya ta daure su: haraji, da kuma rashin cikakken daukar alhaki da ke kewaye da shi. Idan kai matashin Afirka ne, wannan shi ne mafi muhimmanci kan batun da ke tantance makomarka.
An koya mana cewa kakaba haraji na gina hanyoyi da makarantu. Amma me ke faruwa yayin da bashin ya lalace zuwa marar ma’ana da kashe kudaden da ba a bin ba’asi?
Bari mu bayyana karara: Bashi ba shi da muni a kashin kansa. Kasashe suna aro kudade don gina kasa. Lamunin da aka karɓa a shekarun 2000 da 2010 sun kasance na shimfida layukan dogo da tashoshin wutar lantarki.
Amma ga tambayar da matasa ke yi cikin fushi: Ina ayyuka da kayayyakin more rayuwa da ake tsammanin za a gina da kudaden?
Ku kalli kasar Mozambique. Tsakanin 2013 da 2014, wani rukunin jami'an gwamnati sun karɓi bashin sama da dala biliyan 2 daidai da kashi 12 cikin 100 na GDP din kasar daga cibiyar bayar da basussuka ta Credit Suisse da wasu bankuna, waɗanda ake zargin an yi su ne don ayyukan kamun kifi na Tuna da ayyukan sa ido a bakin teku.
An ɓoye kimanin dala biliyan 1.3 har sai da kafofin watsa labarai na duniya suka fallasa satar a 2016.
Bankin Duniya ya rubuta sakamakon ci bayan: ci gaban kasar ya ragu daga kashi 7.7 cikin 100 zuwa kashi 3.3 cikin 100, kuɗin kasar ya faɗi, hauhawar farashi ya karu zuwa kashi 17.4 cikin 100, kuma bashin kasashen waje ya ƙaru daga kashi 61 cikin 100 na GDP zuwa kashi 104 cikin 100. An mayar da Mozambique ta zama kasar da ba ta biyan bashi.
A yau, kashi 73 cikin 100 na kuɗin shigar haraji na kasar yana tafiya ga albashin gwamnati, wani kashi 20 cikin 100 na biyan bashi, wanda ya bar kashi 7 cikin 100 kawai don ayyukan ci gaba. Mutane suna biyan bashin da ba su gina komai ba.
A Kenya, jama'a suna tambaya: ina ci gaban da aka samu daga shekaru goma na aro yayin da yanzu ake buƙatar mu biya ƙarin harajin VAT akan burodi?
Wannan shi ne babban abin da ya haifar da boren matasa. Mun fahimci dole ne a biya lamuni. Amma ba mu yarda mu biya bashin gadoji da suka ruguje ba, hanyoyin da ba su ƙare a ko'ina ba, da kuɗin da aka sace kawai.
Bugu da ƙari, harajin da aka sanya yana da matuƙar kawo koma baya. Suna fi tsananta wa talakawa. Lokacin da gwamnati ta soke haraji ga masu samun kuɗi mai yawa amma ta sanya harajin VAT akan kayayyaki da bayanai masu mahimmanci, wadanda su ne jigon gwagwarmayarmu, sai mu ce an an ayyana yaki kan matasa.
A Najeriya, 'yan kasuwa suna fuskantar tsarin da masu fafutukar matasa suka la'anta a matsayin "tsarin cire kuɗi" wanda ke hana kamfanoni da matasa jagoranci.
A Uganda, masu fafutuka sun yi zanga-zanga tsirara don jawo hankali ga alaƙar da ke tsakanin haraji da cin hanci da rashawa, suna masu cewa "ba tare da haraji mai yawa ba, ba za su sami abin da za su sata ba".
Muna damuwa da haraji saboda mu ne mafi rinjaye. Kashi 70% na al'ummar Afirka suna ƙasa da shekaru 30, duk da haka ayyukan yi miliyan uku ne kawai ake ƙirƙira kowace shekara ga matasa 'yan Afirka miliyan 10 da ke shiga kasuwar neman aiki a kowace shekarar.
Mu ne masu biyan haraji mafi rinjaye. Duk da haka muna da ƙarancin damar shiga ayyukan da harajinmu ke samarwa. Muna biyan kuɗi ga tsarin da bai yi la'akari da abin da ya gabata ba kuma bai saka hannun jari a makomarmu ba.
Kalubalen da ke gabanmu ba wai kawai mu yi zanga-zanga ba ne, sai ma mu sake fasaltawa da sake gina tsarin. Mun tabbatar da cewa za mu iya rufe birane da kuma yada labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta.
Babban aikin da ya fi wahala shi ne ci gaba da wannan kuzarin don gina tsarin da ya fi karfin kowace gwamnati.
Da farko, dole ne mu kafa tsarin da zai tabbatar da cewa an yi adalci. Kin amincewa da Dokar Kudi ta Kenya ta 2024 nasara ce, amma ta wucin gadi. Ba tare da hanyoyin dindindin kamar rajistar da jama'a za su yi na duk bashi ko lamunin da aka karbo da ayyukan da aka yi da su, gwamnatin da ta biyo baya za ta sake gabatar da irin wannan harajin.
Muna buƙatar kwamitocin binciken bashi masu zaman kansu, bin diddigin abubuwan da suka faru kamar binciken basussuka na Ecuador, tare da ikon bincika da kuma kin amincewa da mummunan bashin da aka ciyo ba tare da fa'idantar jama'a ba.
Na biyu, dole ne mu nemi bayyana gaskiya game da kasafin kuɗi kafin a gabatar da sabbin haraji. Bai kamata 'yan Najeriya su yi zanga-zanga ba bayan cire tallafin man fetur don neman ba’asin inda aka ajiye kudaden da aka tanadar. Dole ne a buga kasafin kuɗi ta hanyar da za a iya samun bayansansa cikin sauki kafin a zartar da shi.
Na uku, dole ne mu matsa lamba don samun haraji mai kawo ci gaba. Tsarin da ake da shi a yanzu yana dora nauyi mafi girma ga waɗanda ba su da ikon ɗaukar sa.
Idan gwamnatoci suna buƙatar kudaden shiga, ya kamata su duba waɗanda suka fi amfana daga bashin da suka gabata: manyan kamfanoni, masana'antun haƙo mai, da mutane masu dimbin kudade waɗanda suka biya kuɗi ‘yan kaɗan a tsawon lokaci.
Marubucin, Jon Kafuko, manajan shirye-shirye ne a Kungiyar Youth for Tax Justice Network.