NIJERIYA
2 minti karatu
An yanke wa Sojojin Nijeriya uku hukuncin ɗaurin rai da rai
An yanke wa sojojin hukuncin laifuka da dama, wadanda suka hada da sata, da yin mu’amala da harsasai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma taimaka wa ‘yan ta’adda wadanda duk hukuncinsu ke karkashin dokar kotun sojin Nijeriya
An yanke wa Sojojin Nijeriya uku hukuncin ɗaurin rai da rai
An yanke wa Sojojin Nijeriya uku hukuncin ɗaurin rai da rai bisa laifin sayar da makamai ga 'yan ta'adda
25 Satumba 2025

Wata kotun sojin a Nijeriya ta musamman da ke zamanta a birnin Maiduguri na jihar Borno a Nijeriya ta yanke hukuncin ɗaurin-rai-da-rai ga wasu sojoji uku da kuma wani soji ɗaya da zaman gidan yari na tsawon shekaru 15 bisa samun su da laifin sayar da makamai ba bisa ka'ida ba ga ƙungiyoyin 'yan ta'adda.

An yanke wa sojojin hukuncin laifuka da dama, wadanda suka hada da sata, da yin mu’amala da harsasai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma taimaka wa ‘yan ta’adda wadanda duk hukuncinsu ke karkashin dokar kotun.

Birgediya Janar Ugochukwu Unachukwu, mukaddashin kwamandan runduna ta 7 kuma kwamandan sashi 1, na Operation Hadin Kai (OPHK) ne ya jagoranci shari’ar ta kama mutanen da suka hadar da Raphael Ameh da Sergent Ejiga Musa da kuma Lance Corporal Patric Ocheje da laifin cinikayyar makamai da alburusai tsakaninsu da mayaƙan Boko Haram.

Kazalika kotun ta sami Omitoye Rufus mai rike da muƙamin Corporal da laifin haɗa baki wajen aikata wannan laifi, inda shi kuma aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari.

The court ruled that their actions posed a direct threat to military operations and national security, constituting a clear case of aiding the enemy.

Kotun ta ce laifukan da suka aikata na barazana kai tsaye ga ayyukan soji da kuma tsaron ƙasa, wanda kuma a bayyane yake cewa hakan na taimaka wa maƙiya.

Rumbun Labarai
Gwamnatin Nijeriya ta amince a ci bashin dala 396 domin inganta kiwon lafiya da ayyukan jinƙai
An gabatar da kudiri a Majalisar Dokokin Amurka don saka wa Ƙungiyoyin Miyetti Allah takunkumi
‘Kisan kiyashi ga Kiristoci: Me ya sa kurarin Trump a Nijeriya yake kan kuskure da rashin dacewa?
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince a ɗaure malaman makaranta shekara 14 kan cin zarafin ɗalibai
An kashe 'yan ta'adda fiye da 592 a Borno tun daga Maris din 2025 - Ministan Yada Labaran Nijeriya
ECOWAS ta yi tir da ikirarin ‘ƙarya mai hatsari’ na Amurka cewa Nijeriya ta bari ana kashe Kiristoci
Hukumar DSS a Nijeriya ta kori ma'aikatanta fiye da 100
Amurka na da ajanda a Nijeriya tana fakewa da kisan Kiristoci - Sheik Bala Lau
China na adawa da Trump kan amfani da 'addini da ‘yancin ɗan'adam' domin tsoma baki a Nijeriya
Naira da hannayen-jari Nijeriya sun faɗi sakamakon barazanar da Trump ya yi ta kai hari ƙasar
Jami'an tsaron Nijeriya sun hallaka 'yan bindiga 19 a Jihar Kano
Yadda barazanar da Trump ya yi kan aika sojoji Nijeriya ta tayar da ƙura
Dakarun Nijeriya sun kuɓutar da mutanen da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su Jihar Kogi
Ya kamata Amurka ta taimaka wa Nijeriya da makamai maimakon barazana —Kwankwaso
Muna shirin ɗaukar mataki kan Nijeriya - Sakataren Ma’aikatar Yaƙi na Amurka
Trump ya umarci Ma'aikatar Yaƙi ta Amurka ta soma shirin yiwuwar kai hari Nijeriya
Tinubu ya mayar da martani bayan Amurka ta ce ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta sake jaddada aniyarta ta yaƙi da tsattsauran ra'ayi
Samaila Bagudo: 'Yan bindiga sun sace Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Kebbi
Donald Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake yi wa Kiristoci kisan gilla