| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Tinubu ya bai wa ’yanwasan Nijeriya mata ’yan 17 naira miliyan ɗari-ɗari kan cin Kofin Duniya
Shugaban Nijeriya Tinubu ya bai wa ’yanwasan Nijeriya mata ’yan kasa da shekaru 17 naira miliyan dari-dari saboda lashe Kofin Duniya.
Tinubu ya bai wa ’yanwasan Nijeriya mata ’yan 17 naira miliyan ɗari-ɗari kan cin Kofin Duniya
Flamingos Nigeria / Nigerian Government

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa kowace ’yarwasa ta tawagar Flamingos takardar shaidar ajiyar kuɗi ta Naira miliyan 100, bayan da ƙungiyar ta zama ta farko a Afirka da ta lashe gasar cin kofin duniya ta mata ‘yan ƙasa da shekara 17 ta FIFA.

Uwargidan shugaban ƙasar, Sanata Oluremi Tinubu, ce ta sanar da kyaututtukan a wani liyafar girmamawa da aka shirya a zauren liyafar fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda ta wakilci mijinta.

Babban mai horar da ƙungiyar zai samu kyautar kuɗi har Naira miliyan 100, yayin da kowane mamba na tawagar masu horar da ‘yan wasan zai samu Naira miliyan 50.

Sanata Tinubu ta yabawa ‘yan wasan bisa nasarar da suka samu ta lashe wasanni shida a jere, da kuma ladabi, da biyayya da kuma girmamawar da suka nuna bayan kammala wasan ƙarshe.

Ta ce nasarar za ta zama abin ƙarfafa gwiwa ga ’yanmata masu tasowa, tare da nuna musu cewa za su iya cimma burinsu a fagen duniya.

Ta kuma yaba wa masu horar da ’yan wasan, da ma’aikatan fasaha da na lafiya, da masu gudanarwa, da iyayen ’yan wasan, da kuma magoya baya bisa gudunmawar da suka bayar.

Tawagar ’yan ƙasa da shekara 17 ta lashe kambunta na farko a gasar cin kofin duniya ta FIFA ne bayan ta doke Japan da ci 2-1 a wasan ƙarshe da aka buga ranar 7 ga Nuwamba. Ƙwallayen Awawu Bashiru da Oluebube Umejiaku ne suka tabbatar mata da wannan gagarumar nasara.

Flamingos ta yi rashin nasara da ci 2-1 a wasanta na farko da Poland, amma ta mamaye sauran wasannin, inda ta doke ƙasashe da suka haɗa da Koriya ta Arewa mai riƙe da kambun gasar, da Puerto Rico da kuma Mexico.

Tun bayan nasarar, jami’an gwamnati da magoya bayan ƙwallon ƙafa a sassan duniya sun ci gaba da taya ’yan wasan murna.

Shugaba Tinubu ya kuma taya Flamingos murnar zama ƙungiyar farko a Afirka da ta lashe gasar cin kofin duniya ta mata ’yan ƙasa da shekara 17 ta FIFA.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya ce ya samu labarin nasarar ne bayan dawowarsa daga rangadin kamfen a jihohin Akwa Ibom da Rivers.

Ya bayyana nasarar a matsayin abin alfahari ga Nijeriya, da kuma gagarumar nasara a tarihin ƙwallon ƙafar mata a Afirka.

Shi ma majalisar dattawan Nijeriya ta yi alƙawarin ba Flamingos kyautar Naira miliyan 100.

Alƙawarin ya biyo bayan wani ƙuduri da shugaban kwamitin majalisar kan harkokin wasanni, Sanata Abdul Ningi, ya gabatar, inda ya taya ’yan wasan murna bisa bajintar da suka nuna, tare da yaba wa Hukumar Kwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) bisa rawar da ta taka wajen samun nasarar.

Wannan sabuwar nasara da wata tawagar wasannin motsa jiki ta Nijeriya ta samu ta zo ne ƙasa da shekaru biyu bayan da babbar tawagar ƙwallon ƙafar mata ta ƙasar, Super Falcons, ta lashe kambunta na 10 a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata (WAFCON) a Maroko.

A shekarar 2025 kuma, tawagar ƙwallon kwando ta mata ta Nijeriya, D’Tigress, ta lashe gasar Afrobasket ta mata ta FIBA, inda ta kafa tarihi ta hanyar lashe kambunta na biyar a jere.