Nijeriya na neman tallafin IMF da Bankin Duniya don rage tasirin yakin Iran kan tattalin arziki
Ministan Kuɗi na Nijeriya, Wale Edun, ya ce yaƙin Iran ya yi tasiri da kuma yin barazanar cutar da sauye-sauyen tattalin arziƙin da gwamnatin ƙasar ta fara tun 2023.
Yayin da yaƙin Iran ke ci gaba da tasiri kan tattalin arziƙin duniya, Nijeriya za ta nemi ƙarfafa samun tallafi daga Asusun Lamuni na Duniya, IMF, yayin babban taron IMF da Bankin Duniya, zai fara a wannan makon.
Ministan Kuɗin ƙasar, Wale Edun ya faɗa ranar Litinin cewa yaƙin Iran da Amurka-Isra’ila ya haifar da tashin farasin mai a Nijeriya, sannan yana barazanar kawo cikas kan sauye-sauyen tattalin arziƙin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa a ƙasar.
Duk da cewa Nijeriya na cin moriyar ƙaruwar farashin ɗanyen mai ta hanyan samun kuɗin ƙasashen waje kasancewa ita ce ta fi fitar da man a Afirka, Ministan ya yi tsokani kan batun gabanin taron a birnin Washington DC na Amurka.
Ya ce, "Wannan raɗaɗi na zuwa ne a wata gaɓa mai muhimmanci kuma ya haifar da hauhawar farashin kaya da tsadar rayuwa ga magidanta".
Tun bayan fara yaƙin, a Nijeriya farashin man fetur ya ƙaru da kashi 50% zuwa Naira 1,330 duk lita, yayin da man diesel ya ƙaru da sama da kashi 70% zuwa naira 1,550 duk lita.
Minista Edun ya ce wannan ya yi tasiri kuma yana barazanar cutar da sauye-sauyen tattalin arziƙin da gwamnatin ƙasar ta fara tun 2023, don daidaita ƙasar.
Tuntuni gwamnatin Bola Tinubu ta sauya tsarin tallafin man fetur da kasuwar canjin kuɗi ta ƙasar.
Edun, wanda yake jagorantar kwamitin G24 na ƙasashe masu tasowa, ya ce yana fatan neman bashi mara tsada, da tsarin hada-hadar kuɗi a duniya mai daidaito.