An kashe 'yanta'adda 17 a Nijar tare da kama masu aikata laifuka da masu taimaka musu 33

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa alƙalluman na cikin wata takardar cibiyar haɗa kan ayyukan jami’an tsaron ƙasar (CICO).

By
Kamfanin dillancin labaran ƙasar ta ce jami'an tsaron sun yi nasarar ne tsakanin mako ɗaya / TRT Afrika Hausa

Dakarun tsaron Nijar sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 17 tsakanin ranar 16 zuwa ranar 22 ga watan Fabrairu na shekarar 2026.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa alƙalluman na cikin wata takardar cibiyar haɗa kan ayyukan jami’an tsaron ƙasar (CICO).

Kamfanin ya ruiwaito cewa “waɗannan ayyukan sun ba da damar kashe ‘yanta’adda 17, yayin da aka kama masu laifuka ko kuma masu taimaka wa masu aikata laifuka da ake nema ruwa a jallo guda 33 kuma aka miƙa su ga hukumomin da suka dace.”

Kazalika jami’an tsaron ƙasar sun ƙwace nakiya 1,098 da kilogram 48 na tabar wiwi da lita 23,250 na man fetur da aka samu ta hanyar da ba ta dace ba, da kuma daruruwan miyagun ƙwayoyi.

A cikin watan an ba da rahoton ɗana abubuwan fashewa sau uku inda ƙwararrun jami’ai suka warware biyu daga cikinsu yayin da na ukun ya fashe ba tare da kashe kowa ba, in ji kmafanin dillancin labaran.