| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Iyalai sun yi zanga-zanga a Nijeriya kan yaran da aka sace kusan kwanaki 100 da suka gabata
An sace yaran ne daga ajujuwansu ranar 15 ga watan Mayu a Mussa, wani gari da ke kusa da Dajin Sambisa, wajen da 'yanta'addan Boko Haram suka daɗe suna da ƙarfi a ciki.
Iyalai sun yi zanga-zanga a Nijeriya kan yaran da aka sace kusan kwanaki 100 da suka gabata
Iyaye suna zanga-zanga a Askira-Uba, suna kira da a sake 'ya'yansu, yayin da ɗaliban ke hannun waɗanda suka yi garkuwa da su

Iyayen yaran da aka sace sun yi zanga-zanga a garin Uba na jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya ranar Alhamis, inda suka nemi Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar an sake su kusa kwanaki 100 bayan an yi garkuwa da su.

An sace yaran ne daga ajujuwansu ranar 15 ga watan Mayu a Mussa, wani gari da ke bakin Dajin Sambisa, inda masu ‘yantaddan Boko Haram suka daɗe suna da ƙarfi a ciki.

Zanga-zangar ta jaddada taƙaicin iyalan yayin da garkuwa da mutane ke ci gaba da aukuwa duk da shekaru da aka shafe na ayyukan soji a kan ƙungiyoyuin ta’addanci na Boko Haram da ISWAP da ta ɓalle daga Boko Haram ɗin a arewa maso gabashin Nijeriya.

Yayin da tayar da ƙayar bayan ya ragu, ƙungiyoyin biyu suna kai hare-hare kan fararen hula da makarantu da dakarun tsaro a faɗin jihar Borno da jihohi maƙwabta.

Baya sace yaran ne aka kai hari a garin Lassa da ke kusa ranar 29 ga watan Yuni, inda har yanzu ɗalibai 36 da malami ɗaya ke hannun masu garkuwa da mutane. A watan da ya gabata, hukumomi sun yi nasara ƙwato ɗaliban da ‘yanbindiga suka sace daga makaranta a Jihar oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar, bayan sun shafe watanni biyu suna hannun masu garkuwa da mutane.

'Hankalinmu na tashi kullum'

Wani mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Nijeriya ya ce sojoji “sun kan ƙoƙarin tunkarar matsalar " amma ya ƙi ƙara wani bayani, yana mai tura masu tambayar ga sojoji. Wani mai magana da yawun soji bai yi tsokaci kan buƙatar ƙarin bayani game da lamarin ba.

"Ba mu gan su ba kawo yanzu ," in ji Chinda Buba, wanda ɗansa ke cikin waɗanda aka sace. "Ba mu san inda ‘ya’yanmu suke ba. Ba mu san ko suna cikin ƙoshin lafiya ba ko kuma suna cikin wani mawuyacin hali."

Peace Nicolos, wadda ‘ya’yanta biyu, masu shekaru uku da rabi da takwas da rabi, na cikin waɗanda ake nema, ta ce iyalai suna rayuwa cikin damuwa mara misaltuwa.

"Muna damuwa a ko wace rana kuma da ƙyar muke cin abinci," in ji ta. "Muna roƙon gwamnati ta ceto su."

Orbet Lawan Yakubu, wanda ya wakilci basaraken gargajiya na Mussa, ya ce kawo yanzu ba a san inda kimanin yara 45 suke ba.

"Babu abin da ya fi zafi kamar raba ƙananan yara da iyayensu," in ji shi. "Lamarin ya shafi al’ummar gaba ɗaya saboda kusan ko wane iyali na da dangantaka da waɗanda aka sace."