| Hausa
DUNIYA
4 minti karatu
CIA ta yi shakkar iƙirarin da Isra'ila ta yi kan shirin halaka Trump bayan taron NATO: rahoto
Hukumar ta leken asiri ta yi shakka kan hukumomin leƙen asiri na Isra'ila dangane da barazana ga Shugaban Amurka bayan taron NATO, abin da ya sa shugaban ya shiga wani jirgi a ɓoye, kamar yadda Washington Post ta rawaito.
CIA ta yi shakkar iƙirarin da Isra'ila ta yi kan shirin halaka Trump bayan taron NATO: rahoto
Trump ya ce hukumar Secret Service ce ta ɗauki matakin amfani da wani jirgin saman daban. (AA)

Jami'an leƙen asirin Amurka sun yi shakku kan sahihancin zargin barazanar Iran ta halaka Shugaba Donald Trump, wanda Isra'ila ta fitar kuma ya zama silar aiwatar da wani babban tsarin tsaro yayin barinsa Turkiye a watan da ya gabata, a cewar The Washington Post a ranar Laraba.

Tana ambato jami'an Amurka na yanzu da na baya da suke da masaniya kan bayanan leken asiri, rahoton ya ce masu nazarin CIA ba su dauki bayanan da Isra'ila ta bayar a matsayin masu gamsarwa ba kuma sun bayyana shakkunansu ga jami'an gwamnatin Trump.

Wani jami'in Amurka ya bayyana rahoton cewa 'an samo shi ne daga Isra'ila, ba Amurka ba, kuma an ɗauke shi da matsayin mai rauni,' a cewar the Post.

Wannan damuwar game da bayanan leken asiri ta zama wani sabon bangare na matakan tsaro masu faɗi da aka ɗauka lokacin da Trump ya bar Ankara bayan taron ƙolin NATO a ranar 8 ga Yuli.

The Post a baya ta ruwaito cewa an sauya wa mayar da shugaban jirgi cikin asiri daga jirgin Air Force One zuwa wani jirgi na uku bayan an samu damuwa kan ko sabon jirgin Boeing 747-8 da Qatar ta bai wa Amurka yana da isassun matakan tsaro don tafiyar.

An ce an dauki Trump daga jirgin Air Force One na filin jirgi zuwa jirgin soji C-32A cikin motar kayan abinci ta filin jirgi. Shi da wasu masu taimaka masa ‘yan kaɗan da suka tashi zuwa sansanin jirgin saman Mildenhall na Birtaniya. Jiragen yakin F-16 ne suka yi wa jirgin rakiya .

Matakan kariya na musamman

Fadar White House ba ta mayar da martani kai-tsaye kan tambayoyin game da kimantawar bayanan sirrin ba. Wani jami'in Amurka ya ce shugaban ya fuskanci barazana da dama, ciki har daga Iran, kuma an ɗauki dukkan matakan da suka dace don kare shi.

'Kamar yadda shugaban ya faɗa, ya fuskanci barazana da dama a rayuwarsa, ciki har daga Iran, kuma an ɗauki dukkan matakai don tabbatar da tsaronsa,' wani jami'in Amurka aka zayyano yana cewa a cikin wata sanarwa.

'Babban aikin Jami’an tsaron Secret Service shi ne kare shugaban ƙasa, wanda sun cim ma hakan.'

CIA ta ki yin sharhi, yayin da Ofishin Jakadancin Isra'ila a Washington bai bayar da amsa kan neman bayanai na jaridar ba kai-tsaye.

Duk da tambayoyin game da bayanan leken asiri, jami'an Amurka sun ce a ƙarshe hukumar tsaron Secret Service ta yanke hukuncin cewa barazanar na iya buƙatar matakan kariya na musamman.

'Secret Service ta kusan gamuwa da hatsari sau uku tare da wannan shugaban, don haka ba za su dauki kasada ba,' kamar yadda wani jami'i ya shaida wa The Post.

Trump kansa ya faɗa a ranar Talata cewa shawarar amfani da wani jirgi daban ta fito ne daga jami’an Secret Service.

'Gaskiya duk komai ya rataya ne kan Secret Service. Ni kawai ina bin abin da suke so su yi,' in ji shi, a cewar The Post. 'Suna so in shiga wani jirgi daban, jirgi daban, daidai tsaro... Ina yin abin da suka ce.'

Ana nazari kan dalilan Isra'ila na

Shakku da aka ruwaito sun haifar da tambayoyi kan dalilin da ya sa Isra'ila ta bai Washingon bayanan na sirri da kuma ko an nufi bayanin ne kawai a matsayin gargaɗi ko kuwa ana nufin ya shafi manufofin Amurka.

A cewar The Post, wasu jami'an leken asiri na Amurka na yanzu da na baya sun yi imani cewa rahoton na Isra'ila na iya kasancewa an bayar da shi ne da nufin shafar yanke shawarar Trump da kuma yadda Washington ke kallon yankin.

Wannan 'ya dace da wani babban salo na rahotannin leken asirin Isra'ila wanda wasu jami'ai ke ganin an tsara shi don yin tasiri wajen irin shawarar da shugaban kasa zai yanke,' in ji wani tsohon jami'i da ya san irin wadannan al'amura, a cewar rahoton.

Rahoton ya ƙara da cewa an bai wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio bayanai kan bayanan Isra'ila da kuma aikin da Secret Service ta tsara. A cewar tsohon jami'in da the Post ta ambata, duk da haka Rubio ya hau jirgin na Air Force One.