Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran ta sanar da rufe Mashigar Ruwan Hormuz “sai abin da hali ya yi”, a cewar kafar watsa labarai ta IRIB, mallakar gwamnatin Iran.
Wata sanarwa da kafar watsa labarai ta Islamic Republic of Iran Broadcasting ta fitar, ta ambato rundunar sojin ruwa ta Rundunar Juyin Juya Hali tana cewa duk wani katsalandan daga ƙasashen waje ko kuma yunƙurin samar da “haramtacciyar hanya” a mashigar ruwan zai gamu da martani mai muni.

Ta ƙara da cewa jiragen ruwa da dama sun ƙi bin gargaɗin da aka yi musu na daina kauce wa hanya don bi a hanyar da aka amince da ita.
A cewarta, an hana wani jirgin ruwa wucewa inda aka yi masa harbin gargaɗi bayan ya kashe na’urorinsa tare da jefa tsarin tsaron jiragen ruwa cikin mawuyacin hali.
Rundunar IRGC ta ce ba za ta ƙyale duk wani jirgin ruwa ya wuce ta mashigar ruwan ba sai Amurka ta daina yin katsalandan a mafitar ruwan.
Kazalika ta yi gargaɗi cewa duk wani sabon hari ko keta doka za su fuskanci kakkausan martani, ciki har da hare-hare ta sama kan abin da ta kira sabbin sansanonin maƙiya da ke yankin.
















