| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
1 minti karatu
Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran ta sanar da rufe Mashigar Ruwan Hormuz 'sai abin da hali ya yi'
Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran (IRGC) ta ce an dakatar da duk wata jigila a Mashigar Ruwan Hormuz sakamakon wani lamari da ya shafi wani jirgin ruwan kasuwanci.
Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran ta sanar da rufe Mashigar Ruwan Hormuz 'sai abin da hali ya yi'
Rundunar Juyin Juya Hali ta ce Mashigar ruwan Hormuz za ta ci gaba da zama a rufe sai abin da hali ya yi

Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran ta sanar da rufe Mashigar Ruwan Hormuz “sai abin da hali ya yi”, a cewar kafar watsa labarai ta IRIB, mallakar gwamnatin Iran.

Wata sanarwa da kafar watsa labarai ta Islamic Republic of Iran Broadcasting ta fitar, ta ambato rundunar sojin ruwa ta Rundunar Juyin Juya Hali tana cewa duk wani katsalandan daga ƙasashen waje ko kuma yunƙurin samar da “haramtacciyar hanya” a mashigar ruwan zai gamu da martani mai muni.

Masu AlakaTRT Afrika - Jagoran Addinin Iran ya sha alwashin ɗaukar fansa kan kisan da aka yi wa Ali Khamenei

Ta ƙara da cewa jiragen ruwa da dama sun ƙi bin gargaɗin da aka yi musu na daina kauce wa hanya don bi a hanyar da aka amince da ita.

A cewarta, an hana wani jirgin ruwa wucewa inda aka yi masa harbin gargaɗi bayan ya kashe na’urorinsa tare da jefa tsarin tsaron jiragen ruwa cikin mawuyacin hali.

Rundunar IRGC ta ce ba za ta ƙyale duk wani jirgin ruwa ya wuce ta mashigar ruwan ba sai Amurka ta daina yin katsalandan a mafitar ruwan.

Kazalika ta yi gargaɗi cewa duk wani sabon hari ko keta doka za su fuskanci kakkausan martani, ciki har da hare-hare ta sama kan abin da ta kira sabbin sansanonin maƙiya da ke yankin.

MAJIYA:TRT World and Agencies
Rumbun Labarai
Ministocin ƙasashen Larabawa da na Musulmai sun haɗu a Jordan don ɗaukar matsaya kan Gabashin Ƙudus
Yaƙin Iran na neman karar da makamai masu linzami na Amurka: rahoto
'Yansandan Dubai sun rufe shafukan sada zumunta 103 na bogi a ƙoƙarinsu na yaƙi da zamba
Trump ya buƙaci Iran ta ƙulla yarjejeniya da Amurka ko ta miƙa wuya
Shin za a amince cewa Netanyahu zai girmama yarjejeniyar janyewar Isra’ila baki daya daga Gaza?
Trump ya ce Amurka da Iran za su soma sabuwar tattaunawa a ranar Litinin
Pentagon ba ta da ƙarfin sojin ruwa na kare Isra'ila: Janar ɗin sojin Amurka
Saudiyya ta kammala shirye-shiryen kafa Ƙawancen Tsaron Teku tare da goyon bayan ƙasashe 14
Trump ya ce kwamitin sulhu na Gaza ya yarda Hamas ta ajiye makamai da janyewar Isra'ila daga yankin
Iran ta yi ikirarin lalata jiragen yaƙin F-35 na Amurka a Jordan
Amurka ta kai wa Iran sabbin hare-hare, in ji CENTCOM
Isra'ila ta kashe dala miliyan 46.5 wajen ƙoƙarin sa AI ya yaɗa ra'ayoyinta kan yaƙin Gaza
Amurka da Saudiyya sun kai hari kan ƙungiyar da ke goyon bayan Iran a Iraki
Iran ta ce babu kyakkyawan yanayin da ya dace ta tattauna da Amurka duk da suna musayar saƙonni
Trump ya dakatar da kai wa Iran hari saboda karancin makaman tsaron samaniya — rahoto
An kai wa ma'aikatan jiragen ruwan India hari kusa da mashigar Hormuz
Iran ta yi watsi da tayin tsagaita wuta da Amurka ta yi mata - rahoto
Houthi ta gargaɗi kamfanonin jigilar kaya su guji amfani da tashoshin jiragen ruwa na Saudiyya
IRGC ta Iran ta yi ikirarin kai hari kan jiragen saman Amurka a Jordan
Iran ta kashe sojojin Amurka biyu, yayin da Trump ya ba da umarnin kai mata hare-hare