Fafaroma Leo XIV ya isa Turkiyya a ziyararsa ta farko ƙasar waje, don jaddada zaman lafiyar duniya
An- shirya cewa Fafaroma zai gana da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da ziyartar birane masu girma da kuma tattaunawa kan ayyukan addini.
Fafaroma Leo XIV ya iso Turkiyya a ranar Alhamis don ziyararsa ta farko ta hukuma a kasashen waje bisa gayyatar Shugaban Kasa Recep Tayyip Erdogan, kuma ya jaddada muhimmancin zaman lafiya a duniya tare da fatan cewa ziyarar za ta nuna wannan mahimmanci ga duniya.
Ministan Al'adu da Yawon Bude Ido Mehmet Nuri Ersoy da wasu manyan jami'ai ne suka tarbi fafaroman a filin jirgin sama na birnin Ankara.
A tawagar fafaroman akwai jami'an Vatican, ciki har da Kardinal Pietro Parolin da Arbishọp Paul Richard Gallagher.
Ya yi tafiyar ne a jirgin sama na musamman da kamfanin Italiya ITA Airways ya tanada wanda ke dauke da alamar fafaroma, kuma ya gaisa da fiye da 'yan jarida 70 daga kafafen yada labarai daban-daban da aka yi tafiyar tare da su.
Ya ce yana matukar farin ciki da yi wannan ziyara, yana mai cewa ya dade yana jiran ta saboda muhimmancinta ga dukkan Kiristoci da ma duniya baki daya.
Ya yi nuni da ayyukan da zai gudanar a Turkiyya da Lebanon, inda ya sake bayyana shirinsa na jaddada muhimmancin zaman lafiya ga kowa a duniya.
Haka kuma ya yi kira ga kowa da a hada kai wajen neman zaman lafiya, yana mai cewa duk da bambance-bambancen addini da imani, dan’adam a asali yana da nasaba, kuma yana fatan ya ba da gudummawa wajen ayyukan da ke karfafa zaman lafiya da hadin kan duniya.
Ziyarar ta fara ne da girmamawa ta musamman ga Mustafa Kemal Atatürk a Anıtkabir, kabarin wanda ya kafa Jamhuriyar Turkiyya.
An shirya tarbar hukuma a Majalisar Shugaban Kasa, inda shi da shugaban Turkiyya za su tattauna dangantakar Turkiyya da Vatican da sauran muhimman batutuwan yanki da na duniya, ciki har da halin da ake ciki a Falasdinu.
Ana sa ran za su yi wani taron manema labarai a Cihannuma Hall da ke Cibiyar Kasa ta Tarihi ta Shugaban Kasa a Ankara, wacce ita ce cibiyar karatu ta uku mafi girma a duniya.
A ranar Jumma'a, fafaroma zai gana da manyan limaman Kirista a Katedral na St Esprit a Istanbul, zai ziyarci gidan kula da tsofaffi na Faransa, sannan zai tafi Iznik da helikofta domin wata hidimar addini.
A ranar Asabar zai ziyarci Masallacin Sultanahmet da Cocin Mor Ephrem na Syriac Orthodox, inda zai gana da Fener Greek Patriarch Bartholomeos. Ranar za ta kare da wata hidima a Volkswagen Arena.
Ziyarar za ta kammala ne da hidima ta karshe a Babban Cocin Apostolic na Armeniya sannan komawa zuwa Fener Greek Patriarchate domin tunawa da ranar kafa ta.
Fafaroma zai kasance a Turkiyya daga 27 zuwa 30 Nuwamba, yana ziyartar Ankara, Istanbul da Iznik.