Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gargadi 'yan ƙasar game da karuwar yunkurin kutse cikin asusun banki na mutane ta hanyar tura sakonnin bogi da imel da ke ikirarin sun fito ne daga bankin.
A wata sanarwa da Mukaddashin Daraktan Sadarwa na CBN, Hakama Ali ya fitar, babban bankin ya ce an tsara saƙonnin bogin ne don yaudarar jama'a ta hanyar tura bayanan sirri masu mahimmanci.
A cewar CBN, ana tura saƙonnin ne ta hanyar imel da sauran kafofin yanar gizo waɗanda suke karfafa wa mutane gwiwa tare da ba su damar shiga shafukan da ake zargin suna da alaƙa da masu aikata zamba da ke yada karya da kuma yanke shawara kan manufofi da dai sauransu na bankin.
Bankin ya yi gargadin cewa irin waɗannan bayanai ana samar da su ne don yin kutse cikin asusun banki da kuma yaudarar mutane.
Babban bankin ya shawarci jama'a da su dogara kan bayanai daga amintattun shafinsa na yanar gizo wato www.cbn.gov.ng, kuma su guji shiga shafukan da ba su tabbatar ba ko kuma raba bayanan sirrirsu a shafukan da a tantance sahihancinsu ba.
Kazalika, sanarwar CBN ta bukaci 'yan Nijeriya da su tabbatar da duk wata sanarwa da ta fito daga Babban Banki ta sahihan hanyoyi tare da sanar da duk wani sako na bogi ko shafukan yanar gizo da ba su yarda da su ba ga hukumomin tsaro.
Bankin CBN ya jaddada kudirinsa na kare tsarin kudin jama’a, tare da karfafa matakan tsaronsa na yanar gizo da kuma haɗin gwiwa da hukumomin da suka dace don yaki da zamba ta yanar gizo.
Sanarwar gargaɗin Bankin ta biyo bayan rahotannin da aka yi ta samu game da kutse cikin asusun bankuna a baya-bayan nan, ciki har da na Hukumar Harkokin Kamfanoni (CAC) da kuma binciken da ake ci gaba da yi a Hukumar Kare Bayanai ta Nijeriya (NDPC) kan zargin kutse a bayanai da suka shafi kudaden da ake biya kai tsaye na ayyukan kamfanoni da na gwamnati da kuma na bankin Sterling da sauran hukumomi.















