Turkiyya tana karɓar baƙuncin taron tattaunawa kan alaƙarta da Ƙasashen Afirka

Türkiye ta zama abokiyar haɗin gwiwa mai ɗorewa a yankin kusurwar Afirka, musamman ta hanyar tallafin da take bai wa Somaliya wajen magance ta'addanci.

By
Taron da aka gudanar a Ankara, babban birnin Turkiyya, ya samu halartar manyan mahalarta daga Turkiyya da kasashen Afirka da yawa. / TRT Afrika

Cibiyar Leƙen Asiri ta Kasa ta Turkiyya, MIT ta shirya wata muhimmiyar tattaunawa da ake kira Shirin Tattaunawar Dabarun Turkiyya-Afirka, wadda za a gudanar daga 9 zuwa 10 ga Fabrairu.

Taron da ake gudanarwa a babban birnin Turkiyya, Ankara, ya janyo manyan wakilai daga Turkiyya da kasashen Afirka da dama, ciki har da Somalia, Sudan, Kenya, Habasha, Eritireya, Nijeriya, Masar, Chadi, Afirka ta Kudu, Senegal, da Gambiya.

Shirin na tsawon kwanaki biyu ya haɗa manyan masu jawabi da kwamitocin tattaunawa kan harkokin tsaro na soja, tsaro, makamashi, da sadarwa.

A jawabin buɗe taro, Daraktan MIT Academy, Farfesa Talha Kose, ya ce shirin zai mai da hankali kan abubuwan da ake fuskanta a Afirka a yau.

Kose ya jaddada muhimmancin Afirka a matakin duniya, yana nanata cewa abubuwan da ke faruwa a nahiyar ba na Afirka kaɗai ba ne, suna shafar duniya baki ɗaya.

Kose ya ce Turkiyya ba ta kallon Afirka a matsayin wani waje na yin gogayya, samun karfin iko ko wajen da take son cin wata gajiya ta gajeren lokaci.

Ya ce Turkiyya na kallon kasashen afirka a matsayin abokai da suke da matsayi iri guda, suke da manufofi na bai daya

Ya ce Turkiyya na mai da hankali wajen gina dangantaka bisa ƙa'idar 'Maganin Afirka ga matsalolin Afirka'.

Hulɗa mai tsari

A cikin jawabinsa, Ministan Shari'a na Somalia, Moallim Mahmoud Sheikhali, ya ce wannan tattaunawa ta zo a lokacin da dangantaka tsakanin Afirka da Turkiyya ta kai wani matakin dabaru wanda ke buƙatar zurfi da hulɗa mai tsari.

Ya jaddada cewa alakar Afirka da Turkiyya tarihi ce kuma ta bambanta da irin wadda tsoffin ƙasashen mulkin mallaka na Yamma suka kafa.

An gina su ne bisa girmama juna, amfanin juna, da haɗin gwiwa—ba bisa mulkin mallaka, cin zarafi, ko tilasta wa ba.

A cewar Sheikhali, Turkiyya ta zama abokin da ke kawo daidaito a Yankin 'Horn of Africa' (Yankin Hancin Afirka), musamman ta hanyar goyon bayanta ga Somalia wajen yakar ta'addanci, ƙarfafa tsaron teku, da magance laifukan da suka ketare ƙasashe.

Ya ƙara da cewa Afirka na buƙatar zaman lafiya, kwanciyar hankali, da sahihan haɗin kai, yana mai cewa tsawon lokaci Turkiyya ta kasance abokin ci gaban da duka bangarorin ke cin riba.