Rikicin cikin gida na Jam'iyyar ADC da makomar dimokuraɗiyyar Nijeriya

Babbar jam’iyyar adawar ta rabu gida biyu ne a halin yanzu wato bangaren da Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark ke jagoranta, sai kuma wanda Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ADC ɗin Nafiu Bala Gombe yake jagoranta.

By
Jam'iyyar ADC Nigeria / Others

A fagen siyasar Nijeriya kallo zai koma Abuja yayin da a mako mai zuwa ne wata Babbar Kotun Tarayya da ke babban birnin ƙasar za ta yanke hukunci dangane da rikicin cikin gida na jam’iyyar adawa ta ADC.

Babbar jam’iyyar adawar ta rabu gida biyu ne a halin yanzu wato bangaren da Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark ke jagoranta, sai kuma wanda Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ADC ɗin Nafiu Bala Gombe yake jagoranta.

 Galibin manyan ’yan siyasar kasar suna bangaren David Mark ne cikinsu har da Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar da Tsohon Gwamnan Jihar Anambra Peter Obi da Tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Tsohon Gwamnan Jihar Osun Rauf Aregbesola da sauransu.

 Idan za a tuna a makon jiya ne Hukumar Zaben Kasar (INEC) ta ce babu daya daga cikin bangarorin biyu da ke ikirarin shugabancin jam’iyyar da ta amince da shi. INEC ta ce ta dauki matakin ne bayan samun wani umarni daga Kotun Ɗaukaka Ƙara.

 Banagren David Mark ya mayar da martani ga INEC, inda ya bukaci murabus din Shugaban Hukumar Joash Amupitan nan take kuma ya zargi INEC da yi wa dimukudariyya zagon kasa da kuma tsoma baki a siyasar cikin gidan jam’iyyar.

 Wannan batu yana ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya da zazzafar muhawara a fagen siyasar kasar wacce za ta gudanar da babban zabe nan da ƙasa da shekara daya.

 Akwai wasu manyan ’yan siyasar kasar da ke zargin Shugaban Kasar Bola Tinubu da hannu a wannan sabon rikici na Jam’iyyar ADC, inda suke cewa yana kokarin mayar da kasar ne kan tsarin jam’iyya daya tilo don tabbatar ci gaba da kasancewarsa a kan mulki.

 Ko da yake wannan zargi dai Shugaban Ƙasar ya musanta shi, amma wasu masana harkokin siyasa suna ganin biri ya yi kama da mutum musamman idan aka yi la’akari da abubuwan da suka faru a jam’iyyar adawa ta PDP, suna masu la’akari da kasancewar Ministan Abuja Nyesom Wike wanda har yanzu dan PDP ne da yake cikin gwamnatin Tinubu.
 Masu sharhi sun ce rikicin da bangaren Wike yake yi da uwar jam’iyyar PDP shi ne ya ɗaiɗaita PDP kuma ya sa wasu manyan ’yan siyasa suka fice daga cikinta kuma suka koma ADC.

 Wani masanin shari’a da ke sharhi kan al’amuran yau da kullum a Nijeriya Barista Nasir Said ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa akwai alamun da ke nuna cewa hukunce-hukuncen kotuna ba za su iya warware wannan matsala da ADC ke fama da ita ba, saboda a cewarsa duk bangaren da hukuncin kotu da za a yanke a nan gaba bai yi wa daɗi ba, to zai daukaka ƙara ne kuma haka za a yi ta jan batun har sai ya kai Kotun Ƙoli.

 Barista Nasir ya ce da wuya ADC ta iya warware wannan matsala a cikin watanni biyu ko uku saboda haka ya ce akwai alamun wannan matsala ce za ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa wanda abin da APC wato jam’iyya mai mulki za ta so ya ci gaba da faruwa ke nan.

 Sannan ganin cewa lokaci yana ƙara ƙurewa musamman idan aka yi la’akari da cewa jadawalin zabukan 2027 da INEC ta fitar ya bukaci jam’iyyun siyasar kasar su gudanar da zabukan fidda gwani kafin karshen watan Mayu wato nan da kasa da watanni biyu, masanin shari’ar ya ce rikicin zai jawo cikas sosai kan yadda za a fidda ’yan takara a ADC da sauran shirye-shiryen tunkarar zabukan 2027.

 Idan ADC ba ta yi nasarar magance wannan rikicin cikin gidan da take fama da shi ba cikin kankanin lokaci, shakka babu hakan zai sa kasar za ta koma tamkar babu wata babbar jam’iyyar adawa wacce za ta iya yin tasiri a zaben 2027, a cewar masanin shari’ar.
Wanda ya ce hakan ba zai haifar wa ɗimukuradiyyar ƙasar alheri ba.

Kuma idan har hakan ta tabbata, to za a iya rasa wata jam'iyyar adawa da ta ƙunshi gaggan 'yan siyasar ƙasar masu fatan kawo ƙarshen jagorancin jam'iyya mai mulki a Nijeriya. Da ma dai tuni wasu manyan jam'iyyu biyu a ɓangaren adawa, wato PDP da LP suke fama da irin wannan rikicin cikin gida. Duka wannan na nuna akwai yiwuwar sake sabon lale a tsarin jam'iyyun adawa a Nijeriya kafin tunkarar zaɓukan 2027