| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun ce suna ƙoƙarin ceto shugaban ƙaramar hukumar Bungudu a Zamfara
Bayanai sun nuna cewa 'yanbindiga sun sace shugaban ƙaramar hukumar Bungudu, Nura Umar Abdullahi da iyalansa bayan sun kashe jami'an tsaronsa a harin da suka kai gidansa da sanyin safiyar ranar Asabar.
Sojojin Nijeriya sun ce suna ƙoƙarin ceto shugaban ƙaramar hukumar Bungudu a Zamfara
Sanarwar ta ƙara da cewa 'yanta'addan sun tsere tare da shugaban ƙaramar hukumar zuwa cikin dazukan da ke kusa.

Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce dakarunta na Operation Fansan Yamma sun soma ƙoƙarin ceto shugaban ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara, Nura Umar Abdullahi, wanda ‘yanbindiga suka sace tare da iyalansa da sanyin safiyar Asabar.

Wata sanarwa da jami'in yaɗa labaran rundunar Laftanar Kanar Aliyu Danja ya fitar ranar Asabar ta ce 'yanta’adda “sun yi garkuwa da Honourable Nura Umar Abdullahi da iyalansa ne bayan sun ci ƙarfin jami’an tsaron da ke gadinsa.”

Da samun labarin sai dakarun Operation Fansan Yamma suka bi 'yanbindigar a guje inda suka yi musayar wuta da su, in ji sanarwar.

"Matakin da dakarun suka ɗauka ya tilasta wa 'yanta'addan sun bar biyar daga cikin iyalan shugaban ƙaramar hukumar da suka haɗa da 2 daga cikin ‘ya’yansa da mahaifiyarsa da matarsa da 'yan’uwansa," a cewar sanarwar.

Masu AlakaTRT Afrika - An yi jana'izar manoma 26 da aka kashe a harin 'yanbindiga a Jihar Zamfara a Nijeriya

Sanarwar ta ƙara da cewa 'yanta'addan sun tsere tare da shugaban ƙaramar hukumar zuwa cikin dazukan da ke kusa.

Har wa yau sanarwar ta ce harin ya yi sanadin mutuwar masu tsaron shugaban ƙaramar hukumar da suka haɗa da 'yansanda biyu da ɗan sa-kai ɗaya.

Kazalika an kashe wani farar-hula yayin da yayan shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Bello Umar ya ji rauni yayin harin.

Laftanar Kanar Aliyu Danja ya ce bayan aukuwar lamarin jami'an Operation Fansan Yamma da na 'yansanda da na tsaron farin kaya DSS suna aiki tare domin ceto shugaban ƙaramar hukumar.