Jagoran adawa a Nijeriya, Peter Obi, zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa, wanda hakan ake ganin zai sa tarihi ya sake maimata kansa inda aka samu manyan ‘yan takara uku suka fafata a zaɓen da ya gabata.
An ayyana tsohon gwamnan jihar na Anambra a matsayin ɗan takarar wata sabuwar jam’iyya mai suna Nigeria Democratic Congress (NDC) a ranar Asabar.
An yi wa jam’iyyar rajista a hukumance ne a watan Fabrairu.
Jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) ta zaɓi Shugaba Bola Tinubu a makon da ya gabata domin neman wa’adi na biyu bayan ya samu fiye da kuri’u miliyan 10 a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Sai dai kuma, ‘yan adawar na fama da rikice-rikice, kuma rashin haɗin kai a tsakaninsu na iya bai wa Tinubu nasara cikin sauƙi.
Bayyanar Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar African Democratic Congress (ADC) da kuma Obi a matsayin na NDC ta sake share fagen fafatawa tsakanin ’yan takara uku, wanda zai iya raba ƙuri’un adawa tare da ƙarfafa ƙoƙarin Tinubu na samun wa’adi na biyu na shekaru huɗu.
Tinubu ya lashe zaɓen 2023 da kashi 36.6 cikin ɗari na ƙuri’u. Atiku ya samu kashi 29 cikin ɗari, yayin da Obi ya samu kashi 25 cikin ɗari, sakamakon goyon bayan da ya samu daga ƙungiyar magoya baya ta kafafen sada zumunta mai suna “Obidient Movement”.
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, wanda ya samu fiye da kashi shida cikin ɗari na ƙuri’u a zaɓen da ya gabata, ana sa ran za a ayyana shi a matsayin mataimakin ɗan takarar Obi, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka ruwaito.
Da farko dai, manyan masu ƙalubalantar Tinubu uku sun haɗa kai a wani ƙawance ƙarƙashin jagorancin ADC.
Amma shirin haɗin kan ‘yan adawar ya fara rushewa ne ’yan makonnin da suka gabata lokacin da Obi da Kwankwaso suka sauya jam’iyya suka koma NDC, yayin da magoya bayansu suka fara goyon bayan abin da suka kira tafiyar “OK Movement.”














