| hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Tinubu ya yi alhinin mutuwar Janar Uba da 'yan ta'adda suka kashe a Borno
Shugaban na Nijeriya ya kuma yi magana game da ɗalibai 25 da aka sace a makarantar ‘yan mata ta gwamnati a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi ranar Litinin.
Tinubu ya yi alhinin mutuwar Janar Uba da 'yan ta'adda suka kashe a Borno
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya tura mataimakinsa Kashim Shettima Jihar Kebbi domin jajanta wa iyalan ɗaliban
19 Nuwamba 2025

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya tabbatar da mutuwar Birgediya Janar Musa Uba, wanda ‘yan ta’adda suka kashe a bakin aiki a jihar Borno.

A wata sanarawar da ya fitar ranar Talata, babban mai bai wa shugaban shawara kan watsa labarai Bayo Onanuga, ya ce Tinubu ya bayyana baƙin cikinsa game da rasuwar janar din sojin da sauran jami’ai, tare da miƙa saƙon ta’aziyya ga iayalsansu da rundunar sojin ƙasar.

Rahotanni sun ce mayaƙan ISWAP ne suka kashe Janar Uba bayan sun yiwa wani ayarin sojoji da ‘yan sakai kwanton ɓauna a jihar Borno.

“A matsayi na na babban kwamandan askarawan Nijeriya, na shiga cikin damuwa sosai game da mutuwar sojojinmu da hafoshinmu a fagen fama. Allah Ya bai wa iyalan Birgediya Janar Musa Uba da sauran gwaraza da suka mutu dangana,” in ji Tinubu.

An tura Shettima jihar Kebbi

Tinubu ya kuma yi magana game da ɗalibai 25 da aka sace daga makarantar ‘yan mata ta gwamnati a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi ranar Litinin.

Ya ce garkuwar da aka yi da ɗaliban abin baƙin ciki ne, duk da bayanan sirrin da aka samu a kan yiwuwar harin ɓarayin.

“Abin ɓacin rai ne cewa ‘yan ta’adda sun katse ilimin ɗalibai mata da ba su ji ba basu gani ba. Na umarci jami’an tsaro su ɗauki mataki nan take domin mayar da ‘yan matan jihar Kebbi.”

Shugaban ya yaba wa gwamnan jihar, Mohammed Idris, kan yunƙurin da ya yi na hana aukuwar lamarin.

Tinubu ya kuma tura mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima Jihar Kebbi domin yi wa gwamnatin jihar da iyayen ɗaliban jaje tare da tabbatar musu cewa gwamnatin tarayya tana ɗaukan duk wasu matakai na ganin an dawo da daliban cikin aminci.

Da yake nuna rashin jin daddinsa game da giɓin tsaron da ya janyo garkuwa da ɗaliban, shugaban ya yi kira ga al’ummomi a fadin Nijeriya, musamman waɗanda suke fuskantar matsalolin tsaro, su rinƙa bai wa jami’an tsaron bayanai a kan kari.

Ya ce dakarun tsaro ba za su iya aiki a da kyau ba tare da hadin kan al’ummomi ba.

Shugaban ya yi kira ga shugabannin al’ummomi da ‘yan ƙasa, su taimaka wa jami’an tsaro da bayanai masu amfani domin tallafa wa ayyukansu.

“Hadin kansu yana da muhimmanci a yaƙinmu da waɗannan matsalolin tsaron,” in ji shi.

 

Rumbun Labarai
Jerin lokutan da aka shafe ana shari'ar Nnamdi Kanu, jagoran 'yan a-waren Biafra a Nijeriya
Yadda ta kaya a zaman 'yan majalisar Amurka kan zargin yi wa Kirisotci kisan kiyashi a Nijeriya
‘Yan bindiga sun sace ɗalibai da ma’aikata a wata makaranta a Jihar Neja
Jagoran ƴan-awaren Biafra: Babbar Kotu a Nijeriya ta yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai
'Yan Nijeriya miliyan 45 suna bahaya har yanzu a waje — Ministan Muhalli
Ribadu ya jagoranci wata tawagar Nijeriya mai ƙarfi zuwa Amurka kan zargin kashe Kiristoci a ƙasar
Kotu ta yanke wa wani shugaban ISWAP da ya tsara hare-haren kano na 2012 ɗaurin shekara 20
Tinubu ya ɗaga tafiyarsa tarukan G20 da AU-EU saboda yanayin rashin tsaro da ake ciki a Nijeriya
Majalisar Dattawan Nijeriya ta nemi a ɗauki ƙarin sojoji 100,000 don magance rashin tsaro
Majalisar Dokokin Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis
Gwamnatin Jihar Katsina za ta shirya muƙabala tsakanin Yahya Masussuka da sauran Malaman Musulunci
Babban hafsan sojin Nijeriya ya je Jihar Kebbi ya nemi  a tsaurara neman 'yan matan da aka sace
Gwamnatin Nijeriya ta umarci jami’an tsaro su kuɓutar da ɗalibai mata da aka sace a Jihar Kebbi
Nijeriya tana tattaunawa kan tsaro da Amurka bayan barazanar Trump: Yusuf Tuggar
Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da tallafin jarin N50m ga ɗalibai a fannin ƙirƙire-ƙirƙire
Rikicin PDP: Ɓangaren Wike ya yi watsi da kora yayin da jihohi huɗu ke ƙalubalantar Makinde
‘Yan sandan Nijeriya sun tabbatar da sace ɗalibai ‘yan mata 25 a Kebbi
Sojojin Nijeriya sun daƙile kwanton-ɓauna, sun yi watsi da jita-jitar sace wani janar na soja
Kasafin kuɗin gwamnatin kano na 2026 zai haura naira tiriliyan ɗaya - Gwamna Abba Kabir
Yaya karawar Nijeriya da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo za ta kasance?