Tinubu ya yi alhinin mutuwar Janar Uba da 'yan ta'adda suka kashe a Borno
Shugaban na Nijeriya ya kuma yi magana game da ɗalibai 25 da aka sace a makarantar ‘yan mata ta gwamnati a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi ranar Litinin.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya tabbatar da mutuwar Birgediya Janar Musa Uba, wanda ‘yan ta’adda suka kashe a bakin aiki a jihar Borno.
A wata sanarawar da ya fitar ranar Talata, babban mai bai wa shugaban shawara kan watsa labarai Bayo Onanuga, ya ce Tinubu ya bayyana baƙin cikinsa game da rasuwar janar din sojin da sauran jami’ai, tare da miƙa saƙon ta’aziyya ga iayalsansu da rundunar sojin ƙasar.
Rahotanni sun ce mayaƙan ISWAP ne suka kashe Janar Uba bayan sun yiwa wani ayarin sojoji da ‘yan sakai kwanton ɓauna a jihar Borno.
“A matsayi na na babban kwamandan askarawan Nijeriya, na shiga cikin damuwa sosai game da mutuwar sojojinmu da hafoshinmu a fagen fama. Allah Ya bai wa iyalan Birgediya Janar Musa Uba da sauran gwaraza da suka mutu dangana,” in ji Tinubu.
An tura Shettima jihar Kebbi
Tinubu ya kuma yi magana game da ɗalibai 25 da aka sace daga makarantar ‘yan mata ta gwamnati a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi ranar Litinin.
Ya ce garkuwar da aka yi da ɗaliban abin baƙin ciki ne, duk da bayanan sirrin da aka samu a kan yiwuwar harin ɓarayin.
“Abin ɓacin rai ne cewa ‘yan ta’adda sun katse ilimin ɗalibai mata da ba su ji ba basu gani ba. Na umarci jami’an tsaro su ɗauki mataki nan take domin mayar da ‘yan matan jihar Kebbi.”
Shugaban ya yaba wa gwamnan jihar, Mohammed Idris, kan yunƙurin da ya yi na hana aukuwar lamarin.
Tinubu ya kuma tura mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima Jihar Kebbi domin yi wa gwamnatin jihar da iyayen ɗaliban jaje tare da tabbatar musu cewa gwamnatin tarayya tana ɗaukan duk wasu matakai na ganin an dawo da daliban cikin aminci.
Da yake nuna rashin jin daddinsa game da giɓin tsaron da ya janyo garkuwa da ɗaliban, shugaban ya yi kira ga al’ummomi a fadin Nijeriya, musamman waɗanda suke fuskantar matsalolin tsaro, su rinƙa bai wa jami’an tsaron bayanai a kan kari.
Ya ce dakarun tsaro ba za su iya aiki a da kyau ba tare da hadin kan al’ummomi ba.
Shugaban ya yi kira ga shugabannin al’ummomi da ‘yan ƙasa, su taimaka wa jami’an tsaro da bayanai masu amfani domin tallafa wa ayyukansu.
“Hadin kansu yana da muhimmanci a yaƙinmu da waɗannan matsalolin tsaron,” in ji shi.