Aƙalla mutum 21 sun mutu yayin da wani kwale-kwale ya nutse a Kogin Nilu a arewacin Sudan, in ji gwamnatin jihar da ganau.
Jihar River Nile ta bayyana ranar Alhamis cewa an samo gawarwaki 21 bayan hatsarin tare da bayyana sunayensu inda ta yi gargaɗin cewa ba a san inda wasu fasinjojin suke ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.
Kwale-kwalen na tsallake kogin ne tsakanin ƙauyukan Tayba al-Khawad da Deim al-Qarai, in ji sanarwar gwamnatin jihar.

Sanarwa ba ta bayyana abin da ya janyo hatsarin ba.
Ganau sun shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa kwale-kwalen na ɗauke da mutum 30 yayin da hatsarin ya faru.
Fasinjojin da suka tsira
Ƙungiyar likitoci ta Sudanese Doctors Network ta bayyana a wata sanarwa cewa shida daga cikin fasinjojin kwale-kwalen sun tsira.
Ƙungiyar ta ce lamarin ya bayyana "raunin sufiri ta kogi da kuma rashin ƙananan ababen da ake buƙata na tsaro, tare da rashin hukumomi da kuma tawogogi na ceto na fararen-hula a farkon sa’o’i na faruwar lamarin".
Da yawa daga cikin ‘yan Sudan sun dogara ne kan sufuri ta ruwa hanyar amfani da kwale-kwale masu amfani da inji ɗai-ɗai da matuƙi ɗaya ke jan ko wanne.
Yaƙin Sudan da ake yi ya raba ƙasar tsakanin sojin ƙasar da maƙiyansu, rundunar RSF, lamarin da ya sa aka rufe wasu hanyoyi da kuma tsananin taɓarɓarewar hidima ga jama’a a kuma ababen more rayuwa na jinya da ilimi.















