Aƙalla mutane 21 ne suka halaka lokacin da gobara ta mamaye wani hotal a New Delhi ranar Laraba, a wani lamari da ya zama ɗaya cikin mafi muni da aka gani a babban birnin na indiya.
Da dama cikin waɗanda suka rasu maziyarta ne daga ƙasashen Afirka waɗanda suka zo birnin neman lafiya, kamar yadda jaridar Indian Express da sauran jaridun yankin suka ambata.
Gobara a gine-gine na yawan abkuwa a India, saboda ƙarancin kayayyakin kashe gobara da kuma rashin bin dokokin kare rayuka.
Sanarwar ‘yansandan Delhi ta ce Gobarar ta fara ne da safiya a hotal ɗin Flourish Stay, wanda ke wata unguwa da ke da cunkoso a kudancin birnin.
"Muna baƙin cikin sanar da cewa mutum 21 sun mutu a wannan mummunan lamari," cewar rundunar.
Aikin ceto
Sanarwar ta ce ana ci gaba da ayyukan ceto, inda aka kai fiye da mutum 40 zuwa asibitocin da ke kusa don samun kulawar lafiya.
A ƙarshe an ci ƙarfin gobarar da taimakon motocin kashe gobara takwas.
A wani saƙon ta’aziyya da ya wallafa a shafinsa na X, Firaministan India, Narendra Modi, ya ayyana bala'in da ya faru a matsayin “mai muni”, inda ya ce, "Ina miƙa gaisuwata ga makusantan waɗanda suka rasu”.
Hukumomi sun ƙaddamar da bincike don gano yadda gobarar ta samo asali da kuma batun ko rashin bin ƙa'idojin kariya ya taimaka wajen yawan mace-macen.
Ko a Maris ɗin da ya gabata, wata gobara a wani asibitin gwamnati a gabashin India ta halaka aƙalla mutum 10 majinyata.














